April 21, 2023

​Iran: Ana Samun Ci Gaba A Tattaunawa Da Hukumar IAEA

 

Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran “Mohammed Islami” ya jaddada cewa, ana samun ci gaba a shawarwari da ake yi tsakanin Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa, dangane da ziyarar tawagogin kwararru na hukumar, da kuma tuntubar juna tsakanin kasashen biyu.

“Islami”, wanda yake magana da manema labarai a gefen taron majalisar zartarwa a yau, Laraba, ya yi nuni da cewa, an raba na’urorin radioactive guda 67 ga cibiyoyin kiwon lafiya da asibitoci 210 a duk fadin kasar Iran, yana mai jaddada cewa alkaluman da jami’ai suka bayar ya nuna cewa marasa lafiya miliyan daya da ke dauke da cutar Ciwon daji sun amfana da magungunan da ake samarwa a cikin Iran.

Dangane da yarjejeniyar da Iran ta cimma da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa a watan Maris, da kuma ci gaban da aka samu a shawarwarin da bangarorin biyu suka yi, jami’in ya kara da cewa, an samu babban ci gaba da kuma bin kadun lamurra a tsakanin jami’an Iran da kuma na hukumar, kuma ana ci gaba da tattaunawa da musayar ra’ayi.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Iran: Ana Samun Ci Gaba A Tattaunawa Da Hukumar IAEA”