May 19, 2024

Iran : Ana cigaba da adu’o’i wa Shugaba Ra’isi Da Tawagarsa bayan Hatsarin Jirgi

Kafofin yada labarai na kasar Iran sun rawaito cewar

A Iran gidajen talabijin din kasar na watsa adu’o’I daga masalatai daban daban na kasar a daidai lokacin da ake ci gaba da neman jirgi mai saukar ungulu da ya bata dauke da shugaban kasar da tawagarsa yau Lahadi.

Tun bayan sanar da lamarin ne jama’a suka fara tururuwa zuwa masalatai domin yi wa shugaban kasar Ibrahim Ra’isi da tawagarsa adu’o’I bayan sanar da batan jirgin sama mai saukar ungulu da suke ciki.

Hankalin duniya dai ya karkata kan lamarin da halin da ake ciki a Iran.

Jagora sayyedul ka,id (Dz) ya sanar da cewar ayi aduoin akan lamarin.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Iran : Ana cigaba da adu’o’i wa Shugaba Ra’isi Da Tawagarsa bayan Hatsarin Jirgi”