October 23, 2021

Iran: An Gudanar Da Sallar Juma’a Ta Farko A Tehran Bayan Watanni 20

Daga shafin Hausatv


 

A jiya Juma’a an gudanar da sallar Juma’a ta farko a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, bayan kwashe tsawon watanni fiye da 20, sakamakon bullar cutar corona.

Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, an gudanar da sallar Juma’a a birnin Tehran tare da halartar dubban mutane kamar yadda aka saba yi a lokutan baya, haka nan kuma a sauran biranen kasar an gudanar da sallolin Juma’a, bayan da aka samu saukin yaduwar cutar ta corona a fadin kasar.

Wannan mataki na zuwa nea daidai lokacin da ake gudanar da taron makon hadin kan musulmi na duniya a Tehran karo na 35, tare da halartar manyan malamai dam asana daga kasashen duniya, wanda ya yi dai da makon maulidin manzon Allah (SAW).

Kasar Iran dai na daga cikin kasashen da suka yi fama da cutar corona tun daga farkon lokacin bullar cutar, inda ya zuwa yanzu cutar ta yi ajalin mutane akalla 124,700 a fadin kasar, yayin da kuma yanzu haka akwai mutane fiye da 4400 da suke kwance a asibitoci suna jinyar cutar.

Ya zuwa yanzu kusan mutane miliyan 28 ne suka kammala karbar allurar rigakafin cutar corona zango na biyu a fadin kasar mai mutane miliyan 80, yayin da kuma fiye da rabin mutanen kasar sun karbi allurar rigakafin bangare na farko, kafin karbar bangare na biyu.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Iran: An Gudanar Da Sallar Juma’a Ta Farko A Tehran Bayan Watanni 20”