April 27, 2023
Iran: An Fara Gudanar Da Bincike Kan Kisan Ayatollah Abbas Sulaimani

Ma;aikatar shari’a a kasar Iran ta sanar da cewa, an fara gudanar da kwakkwaran bincike kan kisan babban malami Ayatollah Abbas Ali Sulaimani da aka yi jiya Laraba a arewacin kasar.
Bayanin ya ce, jami’ai daga bangarorin ma’aikatar shari’a da na tsaro, da suka hada da jami’an tsaro na farin kaya da kuma ‘yan sanda masu bincike, sun shiga aiki na hadin gwiwa kan wannan batu.
Shugaban kasar ta Iran Ibrahim Ra’isi ya yi Allawadai da kisan malamin, kamar yadda kuam ya yi kira ga dukkanin bangarori an tsaro da kuma shari’a da su gaggauta daukar kwararan matakai na bincike, domin gano masu hannu a kisan da kuma gurfanar da su a gaban kuliya.
A jiya ne aka kashe Ayatollah Abbas Sulaimani, daga daga cikin malaman addini na kasar Iran, kuma mamba a majalisar kwararru masu zaben jagora ta kasar.
Ahmad Zakari
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un”.. ALLAH (t) ya karbi shahadar Ayatullah Abbas Ali Sulaimani.
Ba shakka koma wa ke da hannu cikin wannan kisa ba zai zamo ɓoyayyen lamari ba cewa ‘hannun maƙiya jamhuriyar musulunci da musulmi’ ya zubar da jinin wannan bawan Allah.
Nufin shine raunata jamhuriyar sannan yin amfani da farfaganda wajen nuna kashe-kashen malaman a matsayin ƙiyayyar al’ummar Iran ga jagorancin musulunci. Waɗannan miyagun mutane sunyi ta ƙoƙarin amfani da shelar yancin mata wajen ƙoƙarin yaƙar hijab da ingiza mai kantu ruwa wa wannan jajirtacciyar al’umma kamar yadda zasu ci gaba da duk kafar da suka samu wajen yaƙar musulunci da manufofinsa kyawawa.
Haƙiƙa na fahumci girman hasarar da maƙiya jamhuriyyar musulunci sukai za kuma su ci gaba da yi tun sa’inda na fahimci gaskiyar kiyaye amanar al’ummar wannan ƙasa mai albarka ga wasicin Manzon Allah (s) da kuma haƙiƙanin sallamawarsu ga Allah (s).
Albishir ga maƙiya:
BA SHAKKA ZAKU GIRBI TOZARCI,ƘASƘANCI DA HASARAR DUNIYA DA LAHIRA.
ALLAH kare jamhuriyar musulunci ta Iran har zuwa bayyanar Imam Mahdi(af)