May 10, 2023

​Iran: A Yanzu Rabon Dalar Amurka A Harkokin Kasuwancin Kasar Da kasashen Waje Ya Ragu Zuwa Kasa Da Kashi 10%

Ministan tattalin arziki sannan kakakin gwamnati kan al-amuran tattalin arziki Ehsan Khandouzi, ya ce a yau kason dalar Amurka a harkokin kasuwancin kasar Iran da sauran kasashen duniya ya ragu zuwa kasa da kasha 10% kuma wannan ma yayi yawa.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a jawabinsa na mako-mako kan harkokin tattalin arziki na kasar a nan birnin Tehran. Khandouzi, ya kara da cewa tun shekara ta 2018 ne bayan da gwamnatin Amurka ta sake dawo da takunkuman tattalin arziki kasar, gwamnati ta kuduri anniyar fidda dalar Amurka a cikin harkokin kasuwanci da tattalin arziki na kasar. Amma a lokacin shirin baya tafiya da sauri, amma bayan zuwan wannan gwamnatin al-amura sun fara tafiya da sauri, har gashi a yau mun fidda dalar Amurka daga cikin harkokimmu har zuwa kasa da kasha 10 %. Kuma zamu ci gaba da ganin mun shafe shi kwata-kwata idan zai yu a cikin harkokimmu.

Ministan ya kara da cewa gwamnatin JMI tana kokarin samar da wasu hanyoyi wadanda zasu maye gurbin dalar Amurka a harkokin kasuwarci da kasashen duniya daga ciki, hade bakunan kasar da na kasashen yankin, daga cikin har da kasar Rasha, wanda nan da wata gudu yan kasuwa na kasar Iran zasu yi mu’amala da bankunan kasar Rasha kamar yadda suke yi a nan gida.

Kuma akwai irin wannan shirin na tahowa da kasashen Omman, Turkiyya da Iraki nan kusa. Daga Karshe ministan ya kammala da cewa ziyarar da shugaba Ra’isi ya kai Siriya ya warware matsalolin yan kasuwan Iran a kasar da dama

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Iran: A Yanzu Rabon Dalar Amurka A Harkokin Kasuwancin Kasar Da kasashen Waje Ya Ragu Zuwa Kasa Da Kashi 10%”