September 13, 2023

​Iraki: Yan Ta’adda Masu Adawa Da JMI Zasu Koma Karkashin Kula Na MDD

 

Ministan harkokin wajen kasar Iraki Fuad Hussain ya ce yan ta’adda masu adawa da JMI wadanda suke da sansanoni a kan iyakar kasar kasashen biyu, za’a maidasu karkashi kula da MDD.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran tanakalto ministan yana fadar haka a ziyarar aiki da ya fara a nan Tehran a safiyar yau Laraba. Ya kuma kara da cewa kundin tsarin mulkin kasar Iraki bata amincewa wata kungiyar ta maida kasar Iraki cibiyar kaiwa wata kasa hare-hare ba.

Kafin haka dai kasashen biyu sun cimma yarjeniya ta ganin an kwance damarar yan ta’addan sannan an wargaza sansanoninsu da suke cikin yankin Kurdistan na kasar Iraki, kafin 19 ga watan Satumba da muke ciki. Kuma idan gwamnatin kasar Iraki ta kasa yin hakan to gwamnatin JMI zata dauki daukin kwace damarar yan ta’addan ta duk yadda ta ga dama.

Kafin haka dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naser Kan’ani a ranar litinin ya kara jaddada cewa gwamnatin kasar Iran ba zata amince da tawaita lokacin da kasashen biyu suka amince a tsakaninsu da kawo karshen samuwar wadannan yan ta’addan a kan iyakar kasar Iran ko da na kwana guda ba.

A nashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Hussain Abdullahiyan ya bayyana cewa al-amiran tsaron kasarsa yana da muhimmanci kuma yana da tabbaci gwamnatin kasar Iraki zata aiwatar da aikawarin kamar yadda kasashen biyu suka amince.

 

©voh

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Iraki: Yan Ta’adda Masu Adawa Da JMI Zasu Koma Karkashin Kula Na MDD”