January 25, 2024

IMAMU ALI (A) HASKEN ALLAH (T) NE MABAYYANI

 Marubuci: Al-Baqir Ibrahim Saminaka

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinƙai…

A zagowar ranar haihuwar shugaban muminai Imam Aliy (A), mu leƙa zuwa ga littafin Allah mai tsarki (Tare da jagorancin malamai) don samo kyakkyawar tsaraba ga ma’abota wilaya. Nazarin wata Aya mai girma: “Ya ku mutane, haƙiƙa hujja ta zo muku daga Ubangijinku, kuma mun saukar a gare ku haske mabayyani” [Nisa’i: 174].

 

A wannan Aya mai girma Allab (T) ya kirayi ɗaukacin mutane, tare da faɗin “Hujja ta zo” ds kuma cewa “Ya saukar da haske mabayyani” Wanda cikin khulasa muna iya gano cewa; Annabin Rahama (S) shi ne matsayin “Hujja” a wannan Aya; Kuma shi ne mafi girman “Hujja”, ko dai saboda shi ya zo da hujja mafi girma (Al-ƙur’ani), ko kuma kasancewarsa “Hujja” a kashin kansa cikakkiyar hujja ta Annabitarsa da kuma kaɗaituwar Allah Ta’ala…

 

“Haske mabayyani” kuwa, ya kasance shi ne Ali (A); Kasancewarsa zaɓaɓɓe kuma mai tsarki, wanda girman al’amarinsa bai ɓoyu mu mutanen da Allah Maɗaukaki ya yi magana da mu ba. Domin Allah (T) ɗin shi da kansa ne ya saukar da shi zuwa gare mu bakiɗaya, kuma ya sanya shi a mabayyani. Ashe kuwa lamarin hasken Allah mabayyani ba abu ne da zai ɓoyu ba!

[Tafirul Ayyashi, a shafi na 457].

 

Haƙiƙa Allah (T) ya sanya Imam (A) ne a “Haske mabayyani” wanda da shi ne za mu gyara hanyarmu shi ne zsi nuna mana, shi ne kuma mai riƙe hannayenmu zuwa ga Allah (T). Dalilin da zai ƙarfafi wannan misdaƙi daga zancen Sadiƙul Aminu (S) Inda ya faɗa wa Imam Ali (A) cewa: “Ya Ali, Na rantse da Allah ba a halicce ka ba face don a bautawa Ubangijinka (Ta dalilinka), kuma sai don a san ilimomin addini ta hanyarka, kuma don a gyara abubuwan da suka ɓaci na tafarki(n Allah T)). Kuma haƙiƙa wanda ya karkace maka ya ɓata, wanda kuma bai shiriyu zuwa gare ka ba ba zai shiriyu zuwa ga Allah Maɗaukakin Sarki ba” [Al-Amaliy Na Shaikh Saduƙ: 495].

 

To wannan shi ne Ali Imaminmu, wanda muke bugun ƙirji da yin alfahari da shi, zuwa gare shi mu ke daɗa jawuwa, koyi da koyarwarsa muke ƙoƙarin kwatantawa… Ina taya ɗaukacin muminai murnar zagowar ranar haihuwarsa (S), tare da roƙon kyawawan addu’o’inku gare ni. Allah Ta’ala ya tabbatar da digadiganmu a bisa Wilayarsa (A) ya raya mu da ikhlasi ya karɓi rayuwarmu a bisa yardarsa ya tashe mu cikin tawagarsa zuwa Aljanna Maɗukakiya.

SHARE:
Makala 0 Replies to “IMAMU ALI (A) HASKEN ALLAH (T) NE MABAYYANI”