August 26, 2021

Imam Sayyid Khamenei (2)

Ci gaba daga rubutun da ya gabata…

KARATUNSA DA WALLAFE-WALLAFENSA

Imam Khamina’i bai wuce shekaru biyar ba ya haxu da babban wansa a makarantar koyon karatun Alqur’ani mai girma, bayan wani lokaci sai aka sanya su a makarantar furamare ta koyon addini (Islamiyya) wadda ake kiranta da suna: Darutta’alim Addini.

Wannan makarantar an samar da ita ne da  taimakon wasu muminai, bayan tsanani da takurawa a zamanin Rida Khan. Manufar samar da makarantar shi ne: Tarbiyyantar da xalibai addini fiye da komai.

A wannan makaranta ana koyar da karatun Alqur’ani mai girma da sauran litattafai, irin su: Hilyatul Muttaqin da Hisabussiyaq da Nisabussibyan qari a kan darusan da ake koyarwa a makarantun furamare.

Bayan da ya gama da matakin furamare a wannan makaranta, sai ya koma karatu da yamma a makarantar gwamnati in da ya samu shedar karatu ta tsaka-tsaki, sannan ya kammala karatunsa na babbar sakandare a tsakanin shekaru biyu, in da ya samu shedar kammala karatun sakandare.

Dangane da matakin karatunsa a fagen ilimin addini kuwa, haqiqa Ayatullahil’uzma sidi Khamina’i (Allah ya ja kwanansa) ya yi bayani da kansa game da hakan, in da yake cewa:

“Mahaifina ya taka gagarumar rawa wajen zava mini hanyar ilimi da kuma malamai, haqiqa ya kwaxaitar da ni kuma ya sanya mini son hanyar.

Lokacin da na shiga karatun darusan addini sai ya zamana tazarar da take tsakani na da mahaifina ta yi nisa sosai (ta kai shekaru 45), qari a kan haka mahaifina ya kasance babban malami ne fitacce, har yana da ijaza ta yin Ijtihadi, sannan ya yaye xaliban ilimin addini da dama a manyan matakai, don haka sai ya zamana irin wannan masayin nasa bai dace a ce yana koyar da ni a matakin farko na karatuna ba, sai dai kwaxayin da yake da shi na tarbiyyantar da mu ya sanya shi tsayuwa ya karantar da mu ni da yayana, daga baya kuma ya karantar da qaninmu. Lallai ya taka muhimmiyar rawa wajen karatar da mu da tarbiyyantar da mu, musamman ni, domin ba don yana nan a raye tare da mu ba da ba mu samu damar samun ilimin Fiqihu da Usul yadda ya kamata ba.

Kafin in je garin Qum na yi karatu da dama a wurin mahaifina, musamman lokacin sanyi, mahaifina ya kasance yana tsara mana lokacin karatu kuma ya karantar da mu da kansa. Wannan dalili ne ya sanya ban sami tsaiko a karatuna ba, savanin sauran xalibai da suke yin karatunsu a hauzozi na gaba xaya, wadda ake yin hutu a lokacin sanyi, da haka ne na kammala karatuna na SUXUH baki xaya, na shiga BAHSULKHARIJ ina xan shekara goma sha shida (16).

Haqiqa gudummawar da mahaifina ya ba ni ta taka rawa wajen ci gaban karatuna, in da matakin karatuna ya xaga nan da nan har na shiga matakin BAHSULKHARIJ a tsawon shekaru biyar da rabi, wato na kammala matakin SUXUH a shekara biyar da rabi.

A shekarar (1957m) na samu ziyarar Atabatul Muqaddasa in da yanayin Hauzar Najaf ya rinqa fuzga ta in zauna a can in nemi ilimi, sai na yanke shawarar zama a Najaf xin, in da na zauna na xan lokaci, sai dai mahaifina bai amince da zamana a can ba, sai na koma Mashhad.

A shekarar (1958m) na je Qum da izinin mahaifina, na zauna a can har sekarar (1964m) (Kimanin shekaru shida ke nan), sai na dawo gida Mashhad sakamakon matsalar ido da mahaifina ya fuskanta duk da rashin amincewa mai tsanani daga wasu malaman Qum”.

Har yau na halarci wani darasin Falsafa a garin Mashhad wurin Ayatullahi Mirza Jawad Tehrani, irin yanayin yadda darasin nasa ya kasace shi ne:Ya kasance yana karantar da Manzuma ne sai ya rinqa karanto darasin marigayi Alhaj Mulla Hadi Sabzawari, sai ya yi masa raddi mai tsanani, haqiqa darasin nasa ya kasance raddi ne ga Manzumar, har xaya daga cikin abokaina da suka karanta Falsafa a Qum ya ce da ni: “Bai dace a ce ka karanta darasin Manzuma a wurin Mirza Jawad ba, domin shi raddi yake yi wa Manzuma kuma da irin wannan ba za ka sami damar fahimtr Hikma ba, don haka ka karance ta a wurin wannan ya yarda da Alhikma”. Sai na gamsu da wannan zance nasa na koma da karatun wurin sheikh Rida Ayisi a Mashhad, ya kasance masani maxaukaki mai hikima kuma ya aminta da dasarin Alhikma sosai, sai na fara xaukan darasin Manzuma a wurinsa, ya kasance yana koyar da darasin cikin qwarewa sosai.

Daga nan sai na koma Najaf, na halarci darusa a wurin Ayat Alhakim da Khu’i da Shahrudi da Mirza Baqir Zanjani da marigayi Mirza Hasan Alyazdi da sidi Yahya Alyazdi, da wasu darusan da ake yi a wasu wuraren daban.

Na amfana matuqa da darasin Ayatullahi Hakim sakamakon irin salon da yake yin amfani da shi da kuma ra’ayoyin da yake bijiro da su na Fiqihu waxanda suke nuna qwarewa.

Sannan kuma na amfana da darasin Ayatullahi Mirza Hasan Bajnudi wanda ya kasance yana karantarwa a masallacin Xusi, na amfana da darasinsa sosai. Sai na yanke shawarar zama a Najaf, sai na rubuta wa mahaifina wasiqa ina neman izininsa game da hakan, sai dai mahaifin nawa bai aminta ba, don haka sai na koma Mashhad.

Bayan wani lokaci sai na je Qum, a nan ne na yanke shawarar zama in karanci kowane irin darasi da yake ba ni sha’awa. A nan na halarci darasin Imam Khomaini (Allah ya gafarta masa), daga nan kuma na halarci wani darasin a wurin Ayatullahil’uzma Burjurdi.

A lokutan da nake halartar dukkan waxannan darsusan na kasance ina halartar darasin Usul a wurin Imam ba tare da yankewa ba, sannan kuma na amfana da darasin Falsafa daga bahasin Xabaxaba’i a darasin Asfar da Shifa’a”.

Sidi Khamina’i ya kai matsayi na Ijtihadi a hannun malaminsa Ayatullahil’uzma Alha’iri a shekara ta (1974m) bayan da ya halarci darasin BAHSULKHARIJ fiye da shekara goma sha biyar.

Ayatullahi Sidi Khamena’i ya shagaltu da yin talifi tun shekarar (1963m), ya wallafa litattafai masu yawa, wasunsu an buga su wasu kuma ba a buga su ba. Ga kaxan daga cikinsu:

Littafin Muntakabul Ahkam

Al’istifta’at (mujalladi biyu ne).

Al’iman.

Attauhid.

Annubuwa.

Al’imama.

Alwilaya.

Bahsun filfikril Islami.

Durusun fima’arifil Islam.

Durusun filfikril Islami.

Alfahmussahih lil’islam.

Durusun fil’aqa’id.

Tafsirul Qur’an.

Alqur’an wal’itra.

Durusun filqur’an.

Almashru’ul’am lilfikril Islami filqur’an.

Durusun filhadis.

Qabasunmin Nahjilbalaga.

Unsurul jihad fihayatil a’immati (a.s).

Alhijra.

Ma’ariful imam Ali (a.s).

Al’imami Ali (a.s) wa’alamuna.

Alhayatus siyasiyyati lil’imam Arrida (a.s).

Asshakhsiyyatus siyasiyyati lil’imam Sadiq (a.s).

Kiraxul jihad (littafin na Bahsulkharij).

Alhukumatu fil Islam.

Durusun fil’akhlaq.

Min’a’amaqissalat.

Bahsun fissabr.

Khasa’isul insanil Muslim.

Su’alun wajawab (mujalladi biyar ne).

Arba’atu kutub rijaliyya ra’isiyya.

Daurul muslimina filhind.

Alfannu Assamin.

Alfannu inda qa’idussaura.

Bahsun fissa’ari.

Tarjamatun fitafsiri Fizilalil Qur’an.

Tarjamatu kitabu sulhul imam Hasan (a.s).

Tarjamatu kitabul mustaqbal lihazaddin.

Tarjamatu kitabu hukmu diddul hadaratul garbiyya.

Jihadul imam Assajad (a.s).

Bahsun fiqhi filhudna.

Bahsun fiqhi fi humsis sa’iba.

Manasikul Hajj.

Alkalimatul qisar.

Asshaikhulmufid wahuwiyyatuttashayyu’i.

Al’audatuila Najulbalaga.

Wani abu mai muhimmaci da ya kamata mu ambata a nan shi ne: Haqiqa sidi Khamina’i ya qware a yaruka masu yawa, kuma ya qware a fannin waqa da adabin Larabci.

 JIHADINSA KAFIN JUYIN-JUYA HALI

A biyo mu a rubutu na gaba…

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “Imam Sayyid Khamenei (2)”