August 27, 2021

Imam Sayyid Ali Khamenei (3)

 JIHADINSA KAFIN JUYIN-JUYA HALI

Cigaba daga runutun da ya gabata…

Babu shakka hauzar ilimi ta Qum ta samu ci gaba ta zama cibiyar ilimi da taqawa da jihadi a shekarar (1962m) sakamakon kiran da imam Khomaini yake yi game da sarki Shah, sai malamai da xalibai suka rinqa yaxa wannan kira nasa. Haka kuma irin yadda imam (Allah ya ji qansa) yake nusasshe da mutane da sauran maraji’ai a kowane lungu na Iran cikin gwarzantaka da qanqan da kai, sai ya kasance aka rinqa yaxa wannan kira nasa ta hanyar bugawa a takardu da taimakon wasu muminai, har wannan fahimta ya game sauran hauzozi da jami’o’i na addini, musamman hauzar Mashhad mai girma, wadda ta tsaya tsayin daka a kan hakan,

Sidi Khamina’i ya taka gagarumar rawa game da wannan fage a gefen al’amuransa da yake gudanarwa a Qum, haqiqa ya kyautata alaqarsa da malamai da kuma xaliban Mashhad.

Ya kuma yi tarayya da malaman Khurasan wajen tanajin xalibai da yanayin da ya dace, ya yi kai-komo qwarai wajen wayar da kan xalibai, ta yadda imam Khomaini ya aika shi a shekarar (1963m) zuwa Mashhad domin ya isar da wasu saqonnin imam guda uku a watan Muharram wanda aka samu ‘intifada’  ranar (15) ga watan Khurdad (a lissafin Shamsiyya).

Imam ya fuskantar da kira na farko zuwa ga malamai da masu Khuxubobi da kuma shugabannin qungiyoyi na addini game da qalubalantar Isra’ila da kuma lamarin Faidiyya. Kira na biyu da na uku kuma ya fuskantar da su ne zuwa ga Ayatullahil’uzma Almilani (Allah ya gafarta masa), wanda ya kasance xaya daga cikin mashahuran malaman Mashhad wanda ya fara bayyanar da qalubalensa a sarari a ranar bakwai da watan Muharram.

Haqiqa sidi Khamina’i ya isar da wannan nauyi da imam ya aike shi da shi yadda ya kamata, kuma wannan ya qara motsa harkar jihadi sosai a yankin Khurasana.

Imam Khamina’i ya rinqa yin kira ga qauyukan da ke kan hanyarsa kafin ya isa wurin da zai kai saqon, kana yana yi musu tsokaci dangane da wannan saqon, da haka ya yi nasarar yaxa yunquri a ko’ina. Daga nan sai ya haxa kan abokan karatunsa da su xaukar wa kawukansu zaga sauran yankuna kuma ya fara a ranar bakwai xin da imam ya sanya, domin yin bayanin halin da ake ciki na daga al’amura na siyasa da na zamantakewa da kuma lamarin makarantar Faidiyya da kuma tsare-tsaren da ake da su game da lamarin, kuma lokaci ne da ya kamata al’umma ta yi wa gwamnatin zalunci tawaye.

Imam da sauran malamai sun amfana da wannan wata na Muharram a wannan shekara qwarai da gaske wajen bayyana wa al’umma halin da ake ciki, tun daga xaya ga watan har ranar shida ga Muharram, daga ranar bakwai kuma aka fara bayyana wa al’umma ko wane ne Shah da kuma irin aikin da yake yi da sunan gyara. A wannan lokaci garin da sidi Khamina’i ya je cibiya ce da ke da qarfin soja wadda ake kira: Birjand yankin zakin Allah, wato firaministan lokacin.

A nan ne sidi Khamina’i ya hau mumbari ya yi bayanin Ashura ga jama’a na ‘yan kwanaki, sai a rana ta bakwai an samu qaruwar jama’a da suka halarci majalisin ya fara jawabi mai ratsa jiki dangane da abin da ya faru a makarantar Faidiyya, a nan ne jama’a suka yi ta kuka da jin wannan cin zarafi da aka yi.

A ranar tara ga watan Muharram kuma sidi ya sake hawa munbari in da ya yi jawabai masu ratsa jiki da motsa al’umma zuwa ga yin qumaji, abin da ya sa nan da nan aka kama shi aka tsare shi.

An tsare shi na tsawon kwanaki goma, bayan da aka sake shi ne sai suka sake haxuwa suka ci gaba da wannan yunquri nasu, suka sake yanke shawarar su qara zaga wasu garuruwan a karo na biyu, domin su ci gaba da tona wa al’umma asirin wannan tsari da yake tafiya a qasar, sannan su sanya wa al’umma ra’ayin yunqurin kawo sauyi, a wannan lokaci kusan muryar malamai ta zo xaya na kiran al’umma su tashi su fafata su yi jihadi.

Wannan kira nasu ya bazu zuwa garuruwa da qauyuka abin da ya tsorata gwamnatin wannan lokaci, a wannan lokacin ne gwamnati ta fito da qarfinta ta tunkari al’umma. Wannan lokaci ya yi daidai da watan Ramalana (1963m), kasantuwar imam ba zai iya gabatar da lamura na Ramalana ba sai makusantansa da sauran xalibai suka tsayu da waxannan ayyuka a sauran garuruwa suna tona qulle-qullen da yake qunshe a cikin wannan tsari.

Sai Ayatullahil’uzma da abokansa suka fara kai komo, kamar yadda ya ambata da bakinsa in da yake cewa: “Lokacin da muka tashi daga Qum a cikin mota, mu talatin ne daga cikin xaliban ilimi kuma kowa da irin aikin da zai yi, haka nan kowa ya rinqa sauka a wurin da zai yi nasa aikin, sai ya zama ni ne mutum na qarshe da zai sauka a Kerman”.

To a Kerman xin sidi Khamina’i ya rinqa yin khuxubobi tare da tattaunawa da malamai da xalibai da mujahidai na tsawon kwanaki uku, sannan ya sake shiga mota ya tafi Zahdan. A can ma ya hau mumbari in da ya haxu da tarba ta jama’a mai ban mamaki, a rana ta shida ne huxubarsa ta sake fita har sai da ya kai ranar goma sha biyar ga watan Ramalana, ranar haihuwar imam Hasan Almujtaba (a.s) in da ya yi huxuba ya motsa al’umma, a nan Safak suka ga cewa babu makawa sai an tsare shi a ranar sha shid ga watan Ramalana.

Sai aka kama shi aka xauke shi  da jirgin sama aka kai shi Tehran da daddare aka tsare shi a gidan sojojin Salxanat Abad, washegari kuma aka canza masa wuri zuwa kurkukun Qarlqal’a, wanda ya shahara da nau’o’in azabtarwa. A nan imam ya share watanni biyu a tsare a xakin da ake tsare mutum xaya, in da suka keta masa alfarma tare da yi masa barazanar kisa da nau’o’in azabtarwa.

Duk da haka abin da wannan gwarzon malamin mai jihadi ya fara yi bayan da aka sake shi daga wannan kurkukun shi ne zuwa ya gana da imam Khomaini (Allah ya gafarta masa) a gidansa da yake Qairaxiyya, kuma ya samu damar ganin nasa ta hanyar sidi Musxafa Khumaini, sun gana na tsawon sa’a guda. Ga abin da yake faxi game da ganawar tasu:

“Babu shakka ganawa da imam ta tafiyar da dukkan gajiyar kurkuku da take tare da ni, har sai da na yi kuka domin farin cikin ganin imam, ya tausaya min qwarai da gaske, har nake cewa da shi: Ba mu amfana da watan Ramalana ba yadda ya kamata sakamakon rashinka, don haka sai mu tanadi watan Muharram mai zuwa tun dag\a yanzu”.

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “Imam Sayyid Ali Khamenei (3)”