September 5, 2021

Imam Ridha Da Sarki Mamun (2)


Waqa a wancan lokacin matsayinta ya yi daidai da kafafen yada labarai, kamar gidan talabishin da radio da jaridu a yau, don haka mahukunta suna qarfafa mawaqa ta hanyar yi musu kyaututtuka.

Sau da yawa akan sami wasu mawaqan da kan danne kwadayinsu ga abin hannun mahukunta su tsaya a gefen gaskiya, ko da kuwa me zai-je-ya-zo, kamar irin yadda Da’abal ya bar yi wa mahukunta waqa ya zabi yi wa iyalan manzon Allah (s.a.w) waqa.
Tarihi ya ambaci haduwar Da’abal Huza’i da imam Rida (a.s). Abu Sultu Alharwi ya ruwaito cewa: Da’abal ya shiga wurin imam (a.s) a garin Maru ya ce da imam (a.s): “Ya dan manzon Allah, na tsara muku waqe, kuma na yi alqawarin cewa babu wanda zai fara jin ta kafin kai”.
Sai imam (a.s) ya yi masa maraba kuma ya gode masa bisa wannan waqe nasa.
Sai ya fara rera wannan waqe mai albarka, daga ciki yake ambaton falalolin Ahlulbaiti da cewa a gidansu ne wahayin Alqur’ani ya sauka, sannan ya rinqa ambaton sunayen wuraren da aka binne kakannin imam Rida (a.s) kamar Kufa da Bagadaza da sauransu yana yabon su, sai imam (a.s) ya yi masa ta’aliqi ya qara masa baiti da irin karin mawaqin, ya ambaci sunan kabarin da ke garin Dus, sai mawaqin ya tambayi imam (a.s) cikin ta’ajibi cewa, wane ne kuma kabarinsa yake Dus? Sai imam (a.s) ya ce da shi: Kabarina ne ya Da’abal.
Sai mawaqin ya ci gaba da ambaton irin masifun da Ahlulbaiti (a.s) suka tsinci kansu a ciki, yana mai tausaya wa imam (a.s), sai imam (a.s) ya rinqa kuka, hawayensa suna zuba.
Da ya gama waqen, sai imam Rida (a.s) ya kawo kyautar kudi dinare dari ya ba shi, sai Da’abal ya qi karba ya nemi imam (a.s) ya ba shi tufafi don ya sami albarkarsa (a.s), imam ya ba shi babbar riga, sannan ya hada masa da dinare dari.
Mawaqin ya karba ya yi wa imam godiya. Yana kan hanyarsa ta komawa gida tare da wasu jama’a sai suka hadu da ‘yan fashi suka tare su, suka qwace musu kudadensu da kayayyakinsu, a lokacin da barayin suke dudduba kayan da suka qwata a gefe sai daya daga cikinsu ya rera wani baitin waqa mai cike da hikima, sai Da’abal ya ji ya tambaye shi cewa: Ko wannan baitin qaqar wane ne?
Sai barawon ya amsa masa da cewa: Waqar Da’abal ce. Sai Da’abal ya ce: Ai ni ne mai wannan waqen. Barayin suka yi mamakinsa kuma suka mayar musu da kayansu don girmamawa gare shi kana suka ba su haquri.
Lokacin da ya isa garin Qum, sai wasu samari suka nemi ya sayar musu da rigar imam Rida (a.s) da dinare dubu (1000), Da’abal ya qi sayar musu, sai suka bar shi, suka rinqa bin sa har sai da ya fita wajen gari suka qwace rigar da qarfi, sai suka kawo dinare dubu suka ba shi kuma suka gutsurar masa wani yanki daga rigar suka hada masa kana ya amince ya tafi.
Da ya isa gida, sai ya tarar da matarsa tana fama da ciwon ido mai tsanani wanda har masu magani sun haqura sun ce makancewa za ta yi, sai Da’abal ya shiga damuwa sosai, sai ya tuna da wannan yanqi na riga imam (a.s), ya fito da shi ya daura mata a fuskarta ta kwana da shi, ko da gari ya waye sai ta tashi garau domin albarkar imam Rida (a.s), kai ka ce ba ita ce take cikin cowon da har an saddaqar cewa makancewa za ta yi ba.

SHAHADAR IMAM RIDA (A.S)
Haqiqa Mamun ya yi matuqar fusata da irin matakan da imam Rida (a.s) yake dauka domin bata duk wani qulli da salon na yaudara da yake fito da shi, sai ya yanke qauna ya fara neman hanyar da zai halaka imam (a.s), duk da kwadaitar da shi mulki da ya yi amma imam bai rudu ba, ya ci gaba da kasantuwa tsattsarka mai gudun duniya.
Ana haka sai Abbasiyyawa da ke Bagadaza suka bayyana tawayensu da barrantarsu ga Mamun, suka nada wani a matsayin halifa maimakon Mamun, don gudun kada halifanci ya koma hannun Alawiyyawa.
Hankalin Mamun ya tashi matuqa, don ya nuna wa ‘yan uwansa Abbasawa yana tare da su ko sa ba shi haxin kai ya ci gaba da halifanci, sai ya yanke hukuncin kama imam Rida (a.s) ya kashe shi, sai aka sanya guba a inibi aka ba shi.
Imam (a.s) ya yi shahada sakamakon wannan guba da ya ci, ya koma ga mahaliccinsa yana abin zalunta shahidi. Shahadarsa ta kasance a shekara ta 203 bayan hijira a garin Dus (Mashhad) wurin da aka binne shi. Tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi.
Kashe imam (a.s) ya qara wa Mamun baqin jini a cikin al’umma kuma sunansa ya qara baci, domin ya wanke kansa kuma ya nuna barrantarsa daga kisan imam Rida (a.s) sai ya bayyana baqin cikinsa bisa wafatin imam (a.s), kuma ya yi tarayya da masu jana’izarsa (a.s) babu takalmi a qafarsa yana kuka.

 

WASU DAGA CIKIN KALMIMINSA (A.S)
1 – Wanda ba ya gode wa iyayensa, ba zai gode wa Ubangiji ba.
2 – Duk wanda ya yi wa kansa hisabi ya ci riba, wanda kuwa ya gafala daga barinta ya yi asara.
3 – Mafificin hankali shi ne mutum ya san kansa.
4 – Idan mumini ya yi fushi to fishinsa ba zai sa shi ya qi gaskiya ba, idan kuma ya so abu to soyayyar ba za ta saka shi ya yarda da barna ba, idan ya yi kintace ba zai dauki fiye da haqqinsa ba.

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “Imam Ridha Da Sarki Mamun (2)”