August 30, 2021

Imam Ridah (AS)

Cigaba da rubutun da ya gabata

TATTAUNAWA DA IMAM RIDA (A.S) A FADAR SARKI MAMUN

Wata rana sarki Mamun ya tara shuwagabannin addinai da malaman mazahabobi ya umarce su da su yi muqabala da imam Rida (a.s), kuma su ruda imam (a.s) da tambayoyinsu. Sai imam (a.s) ya ce da sahabinsa Naufal: “Ka san ko me ya sa sarki mamun ya tara ma’abota shirka?

Sai Naufal ya ce: “Yana so ne ya jarraba ka”.

Sai imam (a.s) ya ce: “Ya Naufal shin kana son sanin lokacin da sarki Mamun zai yi nadama?”

Sai Naufal ya ce: “Na’am”.

Sai imam (a.s) ya ce: “Idan ya ji irin hujjojina ga ma’abota Attaura da Attaurarsu, ma’abota Injila da Injilarsu da ma’abota Zabura da Zaburarsu, su kuwa Sabiyawa da Ibraniyyancinsu”.

Nan imam Ya yi alwala ya nufi fada tare da sahabbansa, aka fara tattaunawa. Sai daya daga cikinsu ana kiransa Jalisiq ya ce: “Ni ba na so a kafa min hujja da Qur’ani domin na tsane shi, haka kuma kada a ba ni dalili da (annabi) Muhammad (s.a.w) don ban yarda da shi ba”.

Sai imam Rida (a.s) ya ce da shi: “Idan na kafa maka hujja da Injila za ka yarda?”

Sai mutumin ya ce: “E na yarda, da shi na yi imani”.

 

Sai imam (a.s) ya karanta masa wani sashe na Injila, inda annabi Isa yake yin bushara da bayyanar wani sabon annabi nan gaba, haka nan ya ba su labarin adadin Hawariyawa, sannan ya karanta masa littafin Ash’aya.

Sai mutumin ya ruxe ya ce: “Na rantse da Isa ban taba zaton a malaman Musulmai akwai irin ka ba”.

Sai imam (a.s) ya fuskanci mutanen Attaura da Zabura su ma ya kafa musu hujja da litattafansu.

Sai Imran sabi faya daga cikin malaman ilimin Kalam ya tambayi imam game da kadaitakar Ubangiji da wasu tambayoyi masu yawa har lokacin salla ya yi, sai imam ya tashi ya yi salla.

Bayan idar da salla sai imam (a.s) ya ci gaba da tattaunawa da Imran har sai da ya sallama wa imam Rida kuma ya yarda da imamancinsa (a.s), sai ya dubi Alqibla ya yi sujjada yana mai bayyana imaninsa da addinin gaskiya.

 

TAFIYA ZUWA MARU

Babu shakka ba wanda ya san haqiqanin dalilin da ya sa sarki Mamun ya zabi imam Rida (a.s) a matsayin mai jiran gadon sarautarsa.

Imam (a.s) yana garin Madina sai halifa ya gayyace shi zuwa garin Maru. Imam (a.s) ya shirya ya nufi Basara, daga nan ya wuce Bagadaza, sannan ya je garin Qum inda aka yi masa babbar tarba, sai imam (a.s) ya sauka a daya daga cikin gidajenta wanda a yau ake kiran wurin da makarantar Radawiyya.

 

GARIN NISABOR

Garin Nisabor dadadden gari ne wanda yake da cibiyoyi na ilmi, daga baya aka ragargaza shi a lokacin yaqin Magul. Mutanen garin sun tarbi imam Rida (a.s) cikin farin ciki, cikinsu har da daruruwan malamai da almajiransu.

Sai malaman suka taru a masaukin imam (a.s) suna dauke da takardu da alqaluma suna jiran imam ya zantar da su wani abu na daga hadisan kakansa (s.a.w), tun kafin ya sauka wasu suka fara riqe ragamar alfadarinsa suna magiya suna cewa: “Don darajar iyayenka masu tsarki ka zantar da mu da wani hadisi da za mu amfana da shi daga gare ka”.

Sai imam (a.s) ya ce: “Na ji babana Musa dan Ja’afar yana cewa: Na ji babana Ja’afar dan Muhammad yana cewa: Na ji babana Aliyu dan Husaini yana cewa: Na ji babana Husaini dan Aliyu yana cewa: Na ji babana Aliyu dan Abi Dalibi yana cewa: Na ji manzon Allah (s.a.w) yana cewa: Na ji mala’ika jibrilu yana cewa: Na ji Allah madaukakin sarki yana cewa: “La’ilaha illallahu birnina ce, duk wanda ya shiga birnina ya kubuta daga azabata”.

Wannan hadisin ya shahara da sunan hadisin sasarin gwal ko hadisin sarqar gwal, kuma adadin wadanda suka rubuta shi sun kai mutum dubu ashirin.

Imam Rida (a.s) ya bar garin Nisabor da safe, suna kan hanyarsu sai lokacin salla ya yi, sai imam ya nemi a ba shi ruwan alwala, sai aka sanar da shi cewa ai babu ruwa.

Nan imam Rida (a.s) ya tona qasa sai ruwa ya bubbugo, ya yi alwala su ma wadanda ke tare da shi suka yi alwalar, gurbin da imam ya tona har yau yana nan.

 

Sai ya isa garin Sana Abad, ya zauna ya jingina bayansa a jikin wani dutse a wurin da mutanen garin suke sassaqa tuqwanen girki, sai ya yi addu’ar Allah ya sanya musu albarka.

Sai imam (a.s) ya shiga gidan Hamid dan Qahdabata Add’i ya shiga wurin da aka binne Haruna Rashid, ya yi rubutu a gefen kabarin cewa:

Wannan ita ce qasata, a nan za a binne ni, kuma Allah zai sanya shi wurin ziyarar ‘Yan Shi’ata, wallahi babu wanda zai ziyarce ni daga cikinsu face Allah ya gafarta masa ya yi masa rahama, ya sanya shi a cikin cetonmu Ahlulbaiti (a.s), sannan ya sallaci wasu raka’o’i, ya yi sujjada mai tsawo, ya yi tasbihi a ciki guda dari biyar.

A biyo mu a rubutu na gaba…

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Imam Ridah (AS)”