August 31, 2021

Imam Ridah (AS) Da Sarki Mamun

IMAM YA ISA GARIN MARU

Ci gaba daga rubutun da ya gabata…

Lokacin da imam Rida (a.s) ya isa garin Maru sai sarki Mamun ya yi masa babbar tarba wadda take nuna dukkan girmamawa. Bayan ‘yan kwanaki da zuwan imam (a.s) sai Mamun ya bigiro masa da batun cewa zai sauka daga kujerar halifanci ya bar wa imam Rida (a.s), sai imam ya qi amincewa da hakan, saboda ya fahimci manufar Mamun game da hakan, kuma yana sane da cewa shi ne ya kashe dan uwansa na jini (qaninsa wanda suke uba daya) Al’amin don ya hau karagar halifanci ta qaqa zai ce zai sauka ya bar wa ni?!

Babu shakka Mamun yana yaudarar al’umma ne ta hanyar bayyana soyayyarsa ga iyalan manzon Allah (s.a.w), don haka ya yi qoqarin tursasa wa imam karbar kujerar mai jiransa gado, don har sai da ta kai shi ga yin barazana da kisa idan imam ya qi amincewa, ta hanyar fadinsa: “Haqiqa Umar Dan Khaddabi ya sanya shura a tsakanin mutum shida ciki har da kakanka Aliyu dan Abi Dalib, kuma ya sanya sharadin cewa duk wanda ya saba daga cikinsu a sare kansa, don haka babu makawa sai ka karvi abin da nake buqata daga gare ka, ba makawa”.[1]

A wata ruwayar kuma cewa ya yi: “… ko da yaushe kana zo min da abin da yake saba min, wallahi sai ka karbi wannan muqamin, idan ba haka zan tursasa ka a kan haka, idan ka qi zan sare kanka”.

Lokacin da imam (a.s) ya ga irin qulle-qullen da ake yi masa sai ya amince, duk da sharaxin da aka sanya na cewa ba zai shiga cikin sha’anin gudanar da mulki ba.

Nan da nan aka buga kudi da sunan imam Rida (a.s), sannan ya sa aka daina sanya baqaqen kaya wadda ta kasance shiga ce ta Abbasiyyawa, suka koma sanya fararen tufafi wadda ta kasnce shiga ce ta Alawiyyawa..

SALLAR IDI

Bayan an yi wa imam Rida (a.s) mubaya’a a matsayin mai jiran gado a ranar (5) ga watan Ramalana, shekara ta (201), bayan kwana ashirin da biyar (25) watan salla ya kama sai Mamun ya ce da imam shi ne zai yi sallar idi da jama’a, imam (a.s) ya ba da uzuri, sai Mamun ya dage kan cewa sai imam ya jagoranci idin wannan salla qarama.

Imam ya amsa amma ya sanya sharadin cewa zai fita sallar da irin yanayin da kakansa manzon Allah (s.a.w) da imam Ali (a.s) suke fita sallar idi. Sai Mamun ya amince,  kuma ya umarci sojoji su yi sammakon zuwa gidan imam (a.s).

Washegari jama’a suka cika hanyoyin da imam zai bi zuwa sallar idi har kan soraye mutane ne, sannan sojoji suka yi sammakon zuwa qofar gidan imam (a.s) suka yi sahu suna jira. Bayan da rana ta haska sai imam (a.s) ya yi wanka ya sanya tufafinsa kuma ya sanya farin rawani, ya saka turare, sannan ya dauki kwagirinsa, ya kuma umarci muqarrabansa da sauran ‘yan rakiyarsa cewa duk abin da ya aikata su ma haka za su yi.

Sai imam Rida (a.s) ya fito babu takalmi a qafarsa, da ya dan yi taku kadan sai ya daga muryarsa ya yi kabbara sai wadanda suke tare da shi su amsa, yayin da sojojin da aka aiko suka gan shi babu takalmi sai suka sauko daga dawakansu suka cire takalmansu.

Idan imam (a.s) ya yi kabbara sai jama’a su amsa, haka nan sautin kabbarori ya dinga dagawa ya cika garin, wadanda ke cikin gidaje suka rinqa fitowa, tituna suka cika maqil da jama’a, suna murna kuma suna nuna sha’awarsu da wannan fitowa ta imam (a.s) wadda ta tuna musu irin yadda manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana fita sallar idi, savanin irin yadda suka saba gani a wurin sarakunansu. Haqiqa wannan fitowa ta imam (a.s) ta motsa musu da ruhin Musulunci, kuma ta zama abar tattaunawa a tsakanin al’umma.

Nan da nan sai ‘yan leqen asirin Mamun suka yi maza suka sheda masa irin abin da ke faruwa na daga irin yadda imam Rida (a.s) ya dauki hankulan al’umma da irin yadda al’umma suke nuna farin ciki gare shi da kuma kyakkyawan ambato da suke yi masa, kuma suka tsoratar da shi cewa irin wannan karvuwar da imam ya ya samu daga al’umma tun daga hanya, suna jin tsoron abin da ka iya fitowa daga bakinsa a lokacin da ya hau kan mumbarin idi ya yi huduba!

Sai Mamun ya tura dan aikensa zuwa ga imam (a.s) da yake kan hanyarsa ta zuwa filin idi, ya sheda masa cewa ya koma kada ya qarasa masallaci. Babu shakka komawar imam (a.s) ta sanya tambayoyi a zukatan jama’a.

MANUFOFIN MAMUN NA DORA IMAM RIDA (A.S) A MATSAYIN MAI JIRAN GADO

Haqiqa babu mai shakkar cewa Mamun yana da kaifin hankali, kuma ya qware a fannin yaudarar siyasa, ya ayyana imam (a.s) a matsayin mai jiran gado ne don ya cimma wani buri nasa na siyasa wanda ya hada da:

1 – Jan hankalin Alawiyyawa wadanda ba su yarda da mulkin daular Abbasiyya ba, kuma suka daga tutocin tawaye a ko’ina, ya jawo hankalinsu ta hanyar dora imam (a.s) a matsayin mai jiran gado, kuma ya sanya fari da koren tufafi a maimakon baqin tufafin da aka san Abbasiyyawa suna sanyawa.

2 -Yaudarar Alawiyyawa ta hanyar ba su muqamai a gwamnati, don al’umma su fahimci cewa da ma mulki suke so ba adalci ba, kuma suna yi wa Abbasiyyawa baqin cikin irin dukiyar da suke da ita, don haka suke neman mulki su azurta kawukansu.

3 – Mamun ya so ya tattara jagororin Alawiyyawa a babban birni ta hanyar nada su muqamai, daga baya ya rinqa saye su daya bayan daya kamar yadda ya nema daga imam (a.s).

4 – Neman amincewar Larabawa gare shi ta hanyar kasantuwar Imam (a.s) a gefensa, ko sa manta da kisan da ya yi wa dan uwansa Al’amin.

Sai dai imam (a.s) yana da cikakkiyar masaniya game da yaudarar da Mamun yake shirya masa, don haka ne ma ya rinqa daukan matakai iri-iri wadanda za su vata shiri ko qullin da Mamum ya yi a qarqashin qasa, kamar irin matakan da imam ya dauka lokacin tattaunawa da shuwagabannin addinai a fadar Mamun, da kuma matakin da ya dauka na lokacin sallar idi, da kuma wanda ya dauka lokacin da aka yi masa mubaya’a da muqamin mai jiran gado kuma aka sharadanta cewa ba zai shiga harkar gudanarwa ba.

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “Imam Ridah (AS) Da Sarki Mamun”