August 26, 2021

Imam Ridah (AS) 2

Cigaba daga rubutun da ya gabata…

Sai wani kuma ya ce: “Wallahi kai ne mafificin mutane”.

Sai imam (a.s) ya amsa masa da cewa: “Kada ka rantse ya kai wannan, wanda ya fi ni shi ne wanda ya fi tsoron Allah madaukaki. Wallahi ba a goge wannan ayar ba: (وجعلناكم شعوبا وقبائل لتعارفوا إن أكرمكم عند الله أتقاكم) ma’ana: Mun sanya ku ku zama al’ummu da qabilu, haqiqa wanda ya fi ku a wurin Allah shi ne wanda ya fi ku tsoronsa.

Wata rana imam Rida (a.s) yana zaune yana amsa tambayoyin mutane game da halal da haram, sai wani mutum xan qasar Hurasana ya shigo ya ce: Amincin Allah ya tabbata a gare ka ya xan manzon Allah, ni mutum ne daga cikin masoyanka da iyayenka da kakanninka, na dawo daga aikin Hajji kuma guzurina ya vata ba ni da komai, ko za ka ba ni abin da zai mayar da ni garinmu, idan na koma zan yi maka sadaka da kwatankwacin abin da ka ba ni, domin ban cancanci a ba ni sadaka ba.

Sai imam ya ce da shi cikin tausayawa: “Zauna Allah ya rahamshe ka”.

Sai imam (a.s) ya ci gaba da sauraren jama’a har suka tafi, sannan imam ya tashi ya shiga xaki, ya miqo hannunsa ta bayan labule ya ce: “Ina mutumin Hurasana?” Sai mutumin ya amsa.

Sai imam (a.s) ya ce da shi: “Ga dinare xari biyu ka yi amfani da su a tafiyarka kuma kada ka yi sadakarsu a madadina”. Sai mutumin ya karva ya yi godiya ya yi sallama da imam ya juya.

Bayan tafiyar mutumin sai imam (a.s) ya fito, sai xaya daga cikin sahabbansa ya ce: “Me ya sa ka voye fuskarka daga barinsa ya xan manzon Allah?”

Sai imam (a.s) ya ce: “Don kada na ga alamun damuwa ko qasqancin tambaya a fuskarsa. Shin ba ka ji faxin manzon Allah (s.a.w) ba ne da ya ce: “Voye kyakkyawan aiki yana daidai da ladan aikin Hajji saba’in, duk wanda kuma ya yake bayyana mummunan aiki tavavve ne, wanda kuma yake voye mummunan aiki abin gafarta wa zunubansa ne”.

WANI KARAMCI NA IMAM RIDA (A.S)

Akwai wani mutum da ake kiransa Ahmad xan qabilar Bizanxi wanda ya kasance xaya daga cikin manyan malamai, suka yi musayar wasiqa da imam Rida (a.s) ya ruwaito wannan hikayar cewa:

Imam Rida (a.s) ya tava gayyatata in zo, sai muka zauna muna tattaunawa, sai ya kawo min abincin dare muka ci, sai ya nuna min makwanci na kwanta shi kuma ya shimfixa mayafi ya kwanta a vari xaya ya kuma rufa da xaya varin.

Sai na ce a raina: Lallai imam ya girmama ni, ruxi ya shige ni. Da gari ya waye muka yi sallama zan tafi, sai imam (a.s) ya riqe hannuna ya ce : ” Haqiqa sarkin muminai Aliyu xan Abi Xalib (a.s)  ya ziyarci Sa’asa’a xan Sauhan don ya duba shi lokacin rashin lafiyarsa, lokacin da imam (a.s) zai tafi sai ya ce da shi: Ya Sa’asa’a kada ka yi alfahari a kan ‘yan uwanka domin na ziyarce ka na zo gaishe da kai”. Imam Rida (a.s) ya fahimci irin saqe-saqen da wannan baqon nasa yake yi, don haka ya yi masa wa’azi, ya ba shi labarin ziyarar kakansa imam Ali (a.s) ga xaya daga cikin sahabbansa.

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “Imam Ridah (AS) 2”