August 22, 2021

Imam Rida (AS)

Daga Mallam Mujtaba Adam

An haifi imam Aliyu Rida a ranar 11 ga watan Zulqi’ida shekara ta 148 bayan hijira a garin Madina mai alfarma. Sunan mahaifinsa imam Musa Alkazim dan imam Ja’afar Assadiq (a.s), sunan mahaifiyarsa Najma, kuma ya rayu tare da mahaifinsa har ya yi wa sahabbansa wasiyya da shi.

Aliyu dan Yaqadini ya ce: Na kasance tare da bawan Allah na gari (Imam Musa (a.s) sai dansa imam Rida ya shigo, sai imam Musa (a.s) ya ce: Ya Ali wannan shi ne shugaban ‘ya’yana. Sai Hashim dan Hakam ya ce: Babu shakka na ba ka labari cewa lamarin yana gare shi bayan imam (a.s).

Wani lokaci kuma daya daga cikin sahabban imam Musa (a.s) ya tambaye shi game da wanda zai gaje shi, sai ya nuna dansa imam Rida (a.s), ya ce: “Wannan shi ne ma’abocinku a bayana”.

Sai dai yanayin zamantakewa da sarakunan wannan zamanin yana da matuqar hadari, don haka imam Alkazim (a.s) ya umarci sahabbansa da boye kansu.

 

DABI’UNSA (A.S)

Imaman Ahlulbaiti zababbu ne wadanda Allah ya zabe su domin shiryar da mutane zuwa gaskiya, don haka suka kasance abin buga misali ga kowane mutum wajen kyawawan halaye.

Ibrahim dan Abbas yana cewa: “Ban taba ganin baban Hasan (imam Rida) ya yi wa wani jafa’i da magana ba, kuma ban taba ganin ya yanke wa wani mutum maganarsa ba har sai ya qare, kuma ban taba ganin ya mayar da mai buqata ba matuqar yana da ikon biya masa ita, bai kuma tava miqe qafarsa a tsakanin abokan zamansa ba ko kuma ya jingina da daya daga cikinsu ko da kuwa bawansa ne.

Ya kasance ba ya kyakyacewa da dariya sai dai ya yi murmushi, idan kuma aka kawo masa abin ci sai ya kira mutane har da bayinsa su hadu su ci, duk wanda ya raya cewa ya ga wani kwatankwacinsa a wajen falala kada ku gasgata shi”.

Wata rana wani ya taba raka imam Rida (a.s) zuwa Hurasana, imam ya sa aka kawo kavaki, sai mabiyansa suka hadu suna ci (ciki har da baqar fata), sai mutumin ya ce: Ya dan manzon Allah da ka ware wa wadannan kwanonsu daban (yana nufin baqar fatar).

Sai imam (a.s) ya ce da shi: “Ai Ubangijinmu guda daya ne shi kadai, kuma ubanmu daya kuma uwarmu daya, sannan kowa za a yi masa hisabi ne da aikinsa”.

Sai wani ya ce da imam (a.s): “Wallahi babu wani a ban qasa da yake da uba madaukaki kamar kai!”

Sai imam (a.s) ya ce: “Shi ma da tsoron Allah ya daukaka”.

Sai wani kuma ya ce: “Wallahi kai ne mafificin mutane”.

 

A biyo mu don cigaba…

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “Imam Rida (AS)”