Imam Khaminae: Makiya Sun Sauya Dabarassu Ta Yakar mutanen Kasar Iran

Kanfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jagoran yana fadar haka a cikin khudubobinsa na sallar Idi a safiyar yau nan birnin Tehran. Ya kuma kara da cewa:
‘A ada, suna amfani da karfin soje don mamayar wata wacce wacce bata dasawa da su, amma a halin yanzu mamayar wata kasa ba zai kaisu ga cimma manufofinsu ba. Don haka a halin yanzu sun koma kan rarraba kan mutane da kuma haddasa rikicin cikin gida, wadanda suka hada da kabilanci da addini da sauransu’.
Jagoran ya kara da cewa a wannan dabarar ma sun kasa kaiwa ga manufarsu a nan kasar Iran, don haka yakamata mutanen su yi hattara, makiya mutanen kasar Iran ba dole ba ne, su yi amfani da dabara ta shekaru goma da suka wuce a kasar a halin yanzu, don sun san ba zasu kai ga manufarsu ba.