April 22, 2023

​Imam Khamenei Ya ce: Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tana Rushewa Da Gaggawa

 

Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) tana rushewa da gaggawa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Imam Khaminae yana fadar haka a yau Asabar, a wata ganawa ta sallar Idi da jakadun kasashen Musulmi a nan Tehran.

Jagoran ya kara da cewa: A Yau muna ganin yadda gwamnatin HKI tace jada baya kadan kadan sannan tana gaggawar gushewa fiye da yadda muke tsammani.

Y ace: Ya zama wajibi ga kasashen musulmi su tallafawa al-ummar Falasdinu don ganin sun ci gaba da kare kansu daga yahudawan Sahyoniyya wadanda suke mamaye da kasarsu fiye da shekaru 70 da suka gabata.

A wabi bangare na Jawabinsa Jagoran ya bukaci hadin kan al-ummar Musulmi ya kuma kara da cewa duk da cewa alkur’ani mai girma ya hanamu rarraba, amma abin bakin ciki a raba muke. Hadin kai tsakanin musulmi wajibi ne don shi ne karfimmu a kan makiyammu.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Imam Khamenei Ya ce: Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tana Rushewa Da Gaggawa”