November 3, 2021

Imam Hasan bn Ali Al-Mujtaba (a.s)

Daga Muhammad Awwal Bauchi


 

A ranar sha biyar ga watan Ramalana mai albarka na shekarar hijira ta uku, gidan Annabci ya sanar da haihuwar jikan farko, nan take sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya garzaya zuwa gidan Fatima (a.s.) don sadar da taya murna da farin cikinsa.

Bayan isowarsa, sai aka gabatarwa Manzo (s.a.w.a) da abin haihuwa mai albarka, Manzo ya tarbe shi, ya dauke shi a hannunsa, ya sumbace shi, ya rungume shi a kirjinsa; sai kuma ya kira salla a kunnensa na dama, ya yi ikama a na hagu da sautin gaskiya da ya zama farkon sautin da ya fara ratsa samuwarsa da jinsa. Sai Manzo (s.a.w.a) ya waiwayi Ali (a.s.) ya ce: “Wane suna ka sa ma dana?” sai Imam Ali (a.s.) ya ce: “Ban kasance mai shiga gabanka ba“, sai Manzo ya ce: “Kamar yadda ban kasance mai shiga gaban Ubangijina ba([1])”. Wannan tataunawa ba ta kai gacinta ba sai ga wahayin Allah na saukowa ga Manzo (s.a.w.a), wanda ke sanar da shi cewa Allah Madaukaki Ya sanyawa abin haihuwan suna Hasan ([2]).

Lokacin da kwanaki bakwai da haihuwa suka kewayo, sai Manzo (s.a.w.a) ya sami rago ya yi masa akika (yankan suna) da shi, daga ciki ya ba unguwar–zoman da ta karbi haihuwarsa  cinya tare da dinari guda, wannan a matsayin godiya bisa kokarinta a madadin abin haihuwa da mahaifiyarsa mai tsarki. Sannan ya kama kan abin haihuwa ya aske, ya yi sadaka da nauyin gashin da azurfa wanda ya yayyafe shi da (wani nau’in turare da ake kira da) Khaluk; sannan ya sa aka yi masa kaciya.

Wannan abu dai da Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi a ranar sunan Hasan (a.s) ya zamanto sunna da musulmi suke koyi da ita.

A biyo mu a rubutu na gaba…

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “Imam Hasan bn Ali Al-Mujtaba (a.s)”