July 28, 2021

IDIN GHADIR: BUKIN CIKAN ADDINI

IDIN GHADIR: BUKIN CIKAN ADDINI

 

Ghadir, wani idon ruwa ne, wanda Allah Madaukaki Ya hukunta wanzuwar ambatonsa. Ya kasance a yankin da aka fi sani da Juhufa,’yan milamilai kadan daga arewa da birnin Makka. Wajen na matsayin wata mararraba ce da hanyoyi suka rarrabu zuwa Masar, Madina, Sham da Iraqi. A wajen ne Mala’ika Jibrilu (AS) ya sauko wa Manozon Allah (SAWA) da wannan saqo na Ghadir.

Ranar da abin ya faru kuwa, ya kasance ranar alhamis, 18 ga watan Zul-Hajji hijirar Manzo na da shekaru goma. A lokacin Maaiki (SAWA) ya ja-gorancin mahajjatan da adadinsu bai kasa dubu dari ba, wadanda suka fito daga garuruwan Musulmi dabam daban. A lokacin sun kammala aikin hajji; kuma sun sami halartar mashhadin nan na ruhi, wanda a cikinsa suka raya wasu ayyuka na uban wannan alumma, wato Annabi Ibrahim (AS); wannan babban mutum da Allah Ya zava kuma Ya dora a muqamin Imamanci, bayan muqaminsa na Annabci; inda har shi kuma ya yi fatan wannan muqami ya ci gaba a cikin tsatsonsa, ya roqi Allah Madaukaki a kan haka, kuma aka amsa masa da kebe wasu daga zuriyarsa da wannan matsayi, kamar yadda ya zo a cikin AlQurani mai girma:

..Lokacin da Ubangijin Ibrahimu Ya jarabce shi da wasu kalmomi, sai (shi Ibrahim) ya cika su. (Sai Ubangiji) Ya ce masa: lallai ni zan sanya ka Imami a kan mutane; (sai Ibrahim) ya ce: har ma da zuriyata; (sai Allah) Ya ce: azzalumai (daga zuriyarka) ba za su sami alqawari na ba (al-Baqara 2:124).

 

Musulmi sun dawo daga wadannan ayyuka na gari da suka ba Annabi Ibrahim daman isar da zababbu daga zuriyarsa matsayin Imamanci, a qarqashin jagorancin daya daga cikin jikokinsa (Manzo SAWA), sai Allah Madaukaki Ya hukunta isar da saqon Ghadir, a matsayin daya daga cikin ma’anonin cika alqawarin da Allah Ya gaya wa Annabi Ibrahim (AS). Allah Ya saukar wa Manzon Sa da saqon cewa:

Ya kai wannan Manzo, ka isar da abin da aka saukar zuwa gareka daga Ubangijinka, idan ba ka aikata (haka) ba, to ba ka isar da (sauran) saqon Sa ba, kuma Allah Zai kare ka daga mutane, lallai Allah ba Ya shiryar da jama’a kafirai.   (al-Ma’ida, 5:57).

Nan take, ba tare da wani bata lokaci ba, sai Manzon Allah (SAWA) ya aika da a tsayar da wadanda ke gabansu, sannan bayan ya cim musu, ya sa a jira wadanda ke baya har sai da suka iso. Sai ya yi horo da kiran Sallah, ya jagoranci mutane Sallar Azahur. Bayan ya kammala sai ya yiwa mutane huduba, wadda yafara da gode wa Allah da yabon Sa. Sannan ya yi wasici, ya tunatar, ya fadi abin da Allah Ya so ya fada, sannan ya ce: An kusa a kira ni in amsa, lallai ni abin tambaya ne, ku ma wadanda za a tambaya ne, shin me za ku ce? Sai duk musulmin dake halarce a wajen suka amsa da cewa:  Mun shaida cewa lallai kai ka isar, kuma ka yi nasiha, Allah Ya saka maka da alheri”. Sai ya ce: Ashe ba ku shaida cewa babu abin bauta (na gaskiya) sai Allah ba, kuma ni Muhammadu bawan Sa ne kuma Manzon Sa, kuma Aljanna gaskiya ce haka wuta gasikya ce ba?” Sai suka ce: “Qwarai kuwa mun shaida.”  Sai ya ce : “Ashe ba ku san cewa ni ne mafi cancantar mai jibintar al’amurran Muminai fiye da su kansu ba?” Sai suka ce: “Qwarai kuwa mun shaida ya Manzon Allah.” Sannan sai ya kama hannun Ali bin Abi Dalib (AS) ya daga sama, har sai da mutane suka ga farin hammatarsu, sannan ya ce:

Duk wanda na zama majibincin al’amarinsa, to Ali ma majibincin al’amarinsa; ya Allah Ka jibinci (lamurran) wanda ya miqa wilaya gare shi Ka kuma bar wanda ya bar shi; Ka kuma taimaki wanda ya taimake shi Ka tabar da wanda ya watsar da shi.

Sannan sai ya ce: Ya Allah ka yi shaida”. Daga nan sai Abubakar (R.A) da Umar (R.A) suka je wajen Ali (AS) suka yi masa san-barka da cewa: “Barkanka! barkanka!! ya dan Abi Dalib, daga yau ka zama majibincin al’amarin kowane mumini da mumina.”

Manzon Allah (SAWA) yana kamala wannan aiki da Allah Ya hore shi a gaban shaidun masu yawa, sai Mala’ika Jibrilu (AS) ya sauko da fadar Allah Madaukaki:

A yau Na cika muku addiniku, kuma Na cika ni’imaTa a kanku, Na kuma yardar muku Musulunci a matsayin addini.  (al-Ma’ida, 5:3).

Wannan shi ne jigon dalilin imanin da ‘yan Shia na gabatar da Aliyu (AS) amatsayin Imami kuma shugaban alummar musulmi bayan Manzon Allah (SAWA), kuma yana layin tarin dalilai da suke tabbatar da haka daga ayoyin AlQurani da suka sauka a kan Aliyu (AS), irin su ayar Sadaukar da Kai (Baqara: 207), ayar turjiyarsa da tabbatansa a imani (al-Maida: 54), fanainsa a taimakon mabuqata (al-Maida: 55-56), yadda Allah Ya kira shi da nafsin Annabi a cikin Ayar Mubahala (Aali Imran: 61) da sauransu na daga ayoyin da wasu malamai suka ce sun kai 300. Qari da maganganun da Manzo (SAWA) ya yi a kansa, wadanda ‘yan Shia suke fahimtarsu a matsayin wasici da shi, kamar kwatanta shi da Haruna a wajen Musa, da cewa shi ne qofar iliminsa, da cewa shi ba ya rabuwa da gaskiya, da cewa shi yana son Allah kuma Allah Yana sonsa da tarin irin su masu yawa wadanda har Imam al-Nasai ya kebe littafi guda a kansu wanda ya kira shi da Khasaisu Amirul-Mu’uminin Aliyu binAbi Talib.

Shi kan shi wannan hadisi na Ghadir, ban da hanyoyin hadisan ‘yan Shia suka fitar kuma suka inganta shi, malamai sun qididdige hanyoyinsa ta bangarorin Ahlul-Sunna, sai suka same shi ya fito ta hanyoyin:

  1. Ahamad bin Hambali: Ya ruwato shi ta hanyoyi 40.
  2. Ibin Jarir Xabari: Ya ruwaito shi ta hanyoyi 72.
  3. Al-Jazri al-Maqari: Ya ruwaiyo shi ta hanyoyi 80.
  4. Ibin Uqda: Ya ruwaito shi ta hanyoyi 105.
  5. Mas’ud al-Sajastani: Ya ruwaito shi da isnadi 1,300.
  6. Shekh Abdullahi ya fada a cikin littafin shi al-Manaqib_ cewa: “Wannan hadisi ya wuce haddin tawatiri, domin babu wani labari da aka xauko ta hanyoyi masu yawa irin na shi.”

Amma adadin wadanda suka kasance tare da Manzon Allah a ranar Ghadir, an yi sabani a kanshi. A wani qauli an ce dubu casa’in, a wani kuma an ce dubu dari da sha hudu ne, a wani an ce dubu dari da ashirin da hudu; wannan shi ne adadin wadanda suka fito tare da Manzon Allah (SAWA). Amma wadanda suka yi aikin haji tare da shi sun fi haka yawa; wato irin wadanda ke zaune a Makka da wadanda suka zo tare da Imam Ali (AS), da wadanda suka zo tare da Abu Musa al-Ash’ari._

Duk da haka, ’yan’uwa  musulmin Ahlul-Suuna ba sa ganin fassarar hadisin Ghadir da yadda ’yan Shi’a suke fassara shi, sai dai suna iya fahimtar cewa imanin ‘yan Shi’a na gabatar da Aliyu (AS)  da shugabantar da shi bayan wafatin Annabi (AS) bai samo asali daga rashin dalili ko hasashe ba. Suna da dalilansu masu qarfi da suka yarda cewa sun ishe su fuskantar kowane irin neman hujja a kan imaninsu da aqidarsu.

Saleh Zariya

26-07-2021

 

 

SHARE:
Makala 0 Replies to “IDIN GHADIR: BUKIN CIKAN ADDINI”