ICC ta ba da sammacin kama Putin kan laifukan yakin Ukraine

Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta ce a ranar Juma’a ta bayar da sammacin kamo shugaban kasar Rasha Vladimir Putin kan laifukan yaki saboda zarginsa da hannu A Ciki.
Kotun ta ce a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce Putin “ana zarginsa da aikata laifin yaki na korar Al’umma ba bisa ka’ida ba da kuma mika yara (yara) daga yankunan da aka mamaye na Ukraine zuwa Tarayyar Rasha ba bisa ka’ida ba.”
Har ila yau, ta bayar da sammacin a ranar Juma’a na kama Maria Alekseyevna Lvova-Belova, kwamishiniyar kare hakkin yara a ofishin shugaban Tarayyar Rasha, bisa irin wannan zargi.
Shugaban kotun, Piotr Hofmanski, ya bayyana a cikin wata sanarwa ta faifan bidiyo cewa, yayin da alkalan kotun ta ICC suka bayar da sammacin, zai rage ga kasashen duniya su aiwatar da shi. Kotu ba ta da rundunar ‘yan sandan kanta da za ta aiwatar da sammaci.
AP 17/3/2023 ✍️