July 28, 2021

HUKUNCIN “GIBA” (CIN NAMA) A KAFAFEN WATSA LABARAI NA ZAMANI A MAHANGAR JAGORA AYATULLAH SAYYID ALI KHAMENEI (DZ)

HUKUNCIN “GIBA” (CIN NAMA) A KAFAFEN WATSA LABARAI NA ZAMANI A MAHANGAR JAGORA AYATULLAH SAYYID ALI KHAMENEI (DZ)

 

A darasin ‘Bahasul Kharij’ da ya ke gabatarwa Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayar da amsa ga tambayar da aka yi masa dangane da giba (cin naman mutum a bayansa ko kuma yi da shi a bayan idonsa) da tabbatuwar hakan cikin lamurra irin su rubutu, shafukan intanet ko kuma daukan haka cikin sauti da hoto da yaxa su. A yayin da yake ba da amsar Jagoran ya yi ishara da wasu abubuwa masu muhimmanci. Ga abin da yake cewa:

 

Lalle babu yadda za a iya cewa wannan aikin (wato giba) ya halalta ko bai halalta ba ko da kuwa da niyyar gyara ce, lalle babu yadda za a iya fadin haka a sake ba tare da wani sharadi ko qarin haske ba. Mu ce shi kenan tun da dai muna so ne mu kawo gyara cikin lamurran al’umma, shi kenan (mu na da haqqin) mu fadi wani abu kan Malam Zaidu da Malam Amru ko kan wancan qungiyar, mu ta fadin maganganu kan su da cin naman su. To a mafi yawan lokuta ma waxannan mutanen da suke yin irin wannan aikin ba sa wadatuwa da gibar kawai, a fili kuna iya ganin hakan. A wasu lokuta su kan zo da wani abin wanda ba a sani ba za a iya kiransa giba ne ko kuma tuhuma, ko qage ko kuma magana ba tare da ilimi ko kuma zage-zage ba. Babu yadda za a ce don dai kawai mutum yana son gyara, to shi kenan hakan ya zamanto halal a gare shi. A’a, kevantattun wajajen da za a iya amincewa da hakan dai su ne wadanda aka yi bayaninsu cikin littafan fiqihu.

 

To sai dai wajibi ne a fitar da wadannan wajaje da kuma tabbatar da su. Wannan lamari ne mai muhimmancin gaske. A haqiqanin gaskiya daya daga cikin wajajen da wajibi ne dukkaninmu mu lura da shi, sannan kuma wajibi ne ma mu gaya wa mutane shi da kuma koyar da su cewa lalle su lura da wannan abu, shi ne: bai kamata daga lokacin da mutum ya ke zaton cewa akwai maslaha cikin lamari shi kenan sai ya dau hannunsa da alqalaminsa ko kuma shafinsa na intanet ya rubuta duk wani abin da ya ke so ko kuma fadin duk wani abin da ya ke so ba, lalle ba haka lamarin ya ke ba. Don kuwa dukkanin wadannan kayayyaki na zamani su ma sun shiga cikin wannan hukumci. Wato karanta shafukan intanet (weblog) kamar karanta takarda ce, ko littafi ko wasiqa ko kuma sauraren wata magana. Sauraren giba ya hada duk wadannan abubuwan; wato akwai mizani na saurare cikin dukkanin wadannan abubuwa. Babu wata siffa kebantacciya da ta kebanci saurare da kunne, karatun wasiqa daidai yake da bahasin da muka yi cikin babin saurare wanda kuma muka jaddada kansa.

 

To ita ma kyamara haka take (wato haka hukumcinta ya ke). A matsayin misali idan mutum ya ga wani ya aikata wani kuskure, sai ya tafi ya dauki hakan da kyamara, sannan kuma ya zo ya nuna wa wani wannan abin, to shi ma dai hakan ya ke, mene ne bambancin su? Lalle wajibi ne a lura da wadannan abubuwa. Wajibi ne mu mai da muhallinmu ya zamanto muhalli da ke cike da kyawawan halaye. Idan har muna son mu gyara al’umma, to ba shi kenan sai mu ta giba da cin naman mutane saboda muna son gyara ba. Akwai wasu hanyoyi na daban (na yin gyarar). To a nan dai na yi magana ne kan giba, ina ga kuma batun tuhuma da qirqirar qarya da makamantan haka.

 

A wani lokaci a baya a lokacin da nake gabatar da wani jawabi da na yi na tava fadin cewa Alqur’ani mai girma yana fadin cewa: “Don me a lokacin da kuka ji shi, muminai maza da muminai mata ba su yi zaton alheri game da kansu ba” (Suratul Nur, 24:12) wato a lokacin da suka ji qaryar da aka qirqira, me ya sa ba su zamanto masu kyakkyawan zato ga junansu ba? Wato tun da farko ma su yi watsi da wancan qaryar. Idan har suka zo suka tuhumi wani mutum, suka fadi wata magana – to ko dai a matsayin tuhuma ko kuma giba – me ya sa kuka yarda da hakan? Ku duba dai wannan kalma ta (Lau la – don me) kalma ce ta jan kunne wacce tana da ma’ana mai girma cikin Alqur’ani mai girma da kuma maganganun larabawa. Ma’anar hakan ba ta taqaita kawai da ‘don me’ wanda muke fadin cewa me ya sa ka yi wannan aiki ba. A nan dai wannan kalma ta ‘Don me’ kalma ce wacce ta ke da ta’akidi (jaddadawa) a tattare da ita. Ma’anar ‘Don me’ ta jan kunne ce. “Don me a lokacin da kuka ji shi, muminai maza da muminai mata ba su yi zaton alheri game da kansu ba” wato me ya sa ba kwa tunanin alheri, me ya sa ba kwa kyakkyawan zato wa junanku. Shi kenan daga wani mutum ya zo (muku da wani labari, ko da ma akwai yiyuwar zaman (maganar ta sa) ingantacciya ce sai ku ce na’am, shi kenan sai mutum ya dauke shi a matsayin yaqini sannan ya dinga yaxa maganar. Hakan dai ba abu ne mai kyau ba, hakan abu ne da aka hana shi. Wannan daya ne daga cikin matsalolin da al’ummar mu take fuskanta a yau, kuma hakan lamari ne da za a iya fahimtarsa daga dalilan da suke tabbatar da giba, hakan ba daidai ba ne; lalle wannan yanayi da muke cikinsa ba daidai ba ne. Ko da yake yin sukan da ta dace da hankali, fadin wadansu maganganu na daidai, wadanda kuma akwai irin waxannan maganganu masu yawa wadanda ambatonsu kawai ba za a iya qirga hakan a matsayin giba ba, sannan kuma mutum yana iya sukan su. Ko shakka babu a yau akwai wata qungiya da take bisa gaskiya kuma ingantacciya, sannan kuma akwai qungiya ta bata wadanda ta kowace hanya suna son su lalata al’ummar mu, su gurvata wannan juyi; babu ko shakka cikin hakan. Akwai kuma wadansu mutane da suke jagorantar wadannan qungiyoyi. Babu ma buqatar sai mutum ya tuhumce su da wani abu. Babu wata buqata ta sai mutum ya yi gibar su. Akwai fitattun maganganun su da yawa wadanda suke a fili; … to komai dai zai fito fili; babu wata buqatar sai an yi da su, ballantana ma wani mutum ya ce sai an yi giba don mu kawo gyara.

 

A saboda haka a ra’ayi na wannan dalilin da muka karanta a babin giba, yana nuna mana dukkanin abin da ake nufi. Wato alal haqiqa wannan shi ne abin da ya kamata mu fahimta daga shari’ar (Musulunci) mai tsarki sannan kuma mu gano shi. Haka nan kuma wajibi ne a yi aiki da shi.

 

Daga:

Muhammad Auwal Bauchi

28/07/202

 

 

SHARE:
Mas'alolin Fiqihu 0 Replies to “HUKUNCIN “GIBA” (CIN NAMA) A KAFAFEN WATSA LABARAI NA ZAMANI A MAHANGAR JAGORA AYATULLAH SAYYID ALI KHAMENEI (DZ)”