Hukumar Zaben Tunusiya Ta Sanar Da Ranar Zabe Zagaye Na Biyu A Kasar

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Tunisiya ta sanar da lokacin gudanar da zaben ‘yan Majalisun Dokokin kasar zagaye na biyu
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Tunisiya a jiya Lahadi ta sanar da cewa: Nan da makonni biyu za a gudanar da zagaye na biyu na zaben ‘yan majalisar dokokin kasar, kuma a yau Litinin ne za a fara yakin neman zaben.
A taron manema labarai da ya gudanar a birnin Tunis fadar mulkin kasar Tunusiya, shugaban hukumar zaben kasar ta Tunusiya Farouk Bouaskar ya bayyana cewa: Za a gudanar da zagaye na biyu na zaben ‘yan Majalisar Dokokin Kasar a ranar 29 ga wannan wata na Janairu, kuma za a fara gudanar da yakin neman zaben ne daga yau Litinin har zuwa ranar 27 ga wata, sannan ranar Asabar 28 babu wanda ke da hakkin gudanar da yakin neman zabe wato jajibere ranar zaben.
Farouk Bouaskar ya kara da cewa: A farkon watan Fabrairu ne za a sanar da sakamakon farko na zaben, kuma sakamakon karshe na zagaye na biyu zai kasance ne bayan kammala daukaka kara, kafin ranar Asabar 4 ga watan Maris.
©Hausa TV.