November 15, 2022

Hukumar zaben kasar Ghana, ta sanar da soke rajistar wasu jami’iyyun siyasar kasar 17, bayan ta tabbatar cewa ba su cika ka’idojin da doka ta tanada ba

Hukumar zaben kasar Ghana, ta sanar da soke rajistar wasu jami’iyyun siyasar kasar 17, bayan ta tabbatar cewa ba su cika ka’idojin da doka ta tanada ba.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta EC ta fitar, ta ce ta soke takardun shaidar jami’iyyun 17, kuma sokewar ta fara aiki tun daga ranar 1 ga watan nan na Nuwamba.
Sanarwar ta kara da cewa, bayan gudanar da cikakken bincike, hukumar zaben ta gano dukkanin jam’iyyun 17, ba su da ofisoshi a matakin kasa ko na jihohi, wanda hakan ya sabawa doka. Hukumar EC ta gudanar da bincikenta ne tsakanin watan Mayu da Yuni, inda ta bukaci dukkanin jam’iyyun kasar su nuna shaidar wanzuwar su, amma wadannan jam’iyyu 17 sun gaza cika wannan sharadi, wanda hakan ya haifar da soke su baki daya.

©cri(Saminu Alhassan)

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Hukumar zaben kasar Ghana, ta sanar da soke rajistar wasu jami’iyyun siyasar kasar 17, bayan ta tabbatar cewa ba su cika ka’idojin da doka ta tanada ba”