September 12, 2021

Hukumar Soji Zata Yi Bancike Kan Kisan ‘Dan Tasi A Jos

Daga Ismail Ali

Runduna ta musamman da ke gudanar da aiyukan dawo da zaman lafiya a jahar filato ta samar da kwamitin da zata yi bincike kan kisan direban tasi mai suna Abdullahi Karafa wanda ake zargin sojoji sun kashe a Jos.

Mejo Ishaku Takwa jami’in yada labarai na hukumar ne ya bayyana hakan a wani bayanin sa a garin Jos a jiya Asabar.

Direban tasi din dai ya kasance mazaunin unguwar Rimi dake arewacin Jos na jahar filato kuma an shaida cewa jami’an soja ne suka yimasa mummunar duka a unguwar Farin Gada wanda hakan yayi sanadin mutuwar sa har lahira.

Bayanai sun nuna cewa mamacin ya samu wannan hukunci ne sanadin laifin da ya aikata na karya dokar kulle wanda take farawa daga karfe 10 na dare.

Jami’in yada labaran ya bayyana cewa kwamandan su Mejo Janar Ibrahim Ali ya ziyarci iyalan mamacin ya kuma basu tabbacin cewa duk sojan da suka samu da hannu cikin wannan danyen aiki zai fuskanci fishin hukuma.

Ya bayyana kuma cewa lamarin ya girgiza su kuma tuni sun nada kwamitin bincike kan lamarin don zakulo wadanda suka aikata wannan danyen aikin.

Jami’in ya ce kwamandan nasu ya gargadi jami’an da kada su rika fita daga iyakokin doka yayin gudanar da aiyukan su, kuma ya gargadi su cewa duk wanda ya tsallake iyakar doka yayin gudanar da aikin to baza su kyale shi ba.

Kana kuma ya tabbatar wa al’ummar gari cewa hukumar su zata rika aiyukan ta bisa kiyaye dokoki, daga bangare guda kuwa gwamnatin jahar filato ta sanya dokar kulle na dukka a yankin bayan faruwar lamarin.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Hukumar Soji Zata Yi Bancike Kan Kisan ‘Dan Tasi A Jos”