October 16, 2021

Hukumar NSCDC ta cafke makiyayin da ya farmaki manomi da makami

Daga Shafin kamfanin dillancin labarai (NAN)

Hukumar “Civil Defence” ta bayyana cewa ta damke wani makiyayi da ya farmaki manomi dan shekara 16 da makami.

Makiyayin mai suna Buji Juli ya farmaki wani manomi mai suna Abubakar Sule inda ya yanke shi a hannu bayan wata yar gajeriyar sa’in’sa da ta shiga tsakanin su a karamar hukumar Kaiama ta jihar Kwara.

Mai magana da yawun hukumar, Babawale Afolabi a wani bayani da yayi a yau Asabar a garin Ilorin ya bayyana cewa farmakin da makiyayin ya kai a manomin na da alaka da sabanin da ke tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar.

 

Jami’in ya bayyana cewa an kai korafi ofishin “Civil Defence” na yankin kan cewa wasu dangi sun farmaki wata dangi na daban wanda hakan ya yi sanadin sarar Abubakar Sule a hannu inda kuma ba tare da wani bata lokaci ba jami’an su suka kama masu alhakin aikata hakan.

Jami’in ya kara da cewa wanda raunata din an kaishi asibitin gwamnati na yankin kana kuma an cigaba da gudanar da bincike kan lamarin.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Hukumar NSCDC ta cafke makiyayin da ya farmaki manomi da makami”