April 5, 2023
Hukumar NDLEA ta kulla alaka da hukumar Kwastam a Nigeriya.

ranar talata 4 ga wata hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta tarayyar Najeriya da hukumar kwastam sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da zai yi sanadin asara mai yawan gaske ga dillalai masu safarar miyagun kwayoyi cikin kasar.
Shugaban hukumar NDLEA mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi Buba Marwa da Kwanturola Janar na hukumar kwastam Hameed Ali sun sanya hannu kan yarjejeniyar ne a birnin Abuja yayin wani kwarya- kwaryar taro.