September 28, 2021

Hukumar “Navy” Ta Nesanta Kanta Daga Kalaman Cmmd. Jamila Kan Sojojin Chadi

Daga Muhammad Bakir Muhammad


Hukumar sojan ruwa a Najeriya wato “Navy’ ta nesanta kan ta daga kalaman zargin da jami’arsu Commodore Jemila Sadiq ta yi kan sojojin Chadi na sayar da makamai ba bisa ka’ida ba.

 

Kamar yadda muka wallafa a shafinmu, jami’ar dai ta yi bayanin ne yayin wani taro da majalisar wakilai ta shirya kan lamarin tsaro. Cikin bayanin nata ta bayyana cewa makaman da manyan kasashen duniya ke bayarwa tallafi ga kasashen ketare na kara rura wutar matsalolin tsaro da ake fama da su a Najeriya.

Ta bayyana dalilin ta kan hakan, inda ta ‘ve yawancin kasashen basa da wuraren adana makamai wanda hakan na sabbaba kasancewar makamai a hannayen jami’an tsaro fiye da kima inda suke amfani da wannan damar su sayar da makaman a yayin da suka tsinci kansu cikin matsin tattalin arziki.

 

Biyo bayan jawabin nata, a yau Talata ne mai magana da yawun hukumar sojin ruwa, Suleiman Dahun ya bayyana cewa wancan bayanin ba da yawun hukumar “Navy” ba ne, fahimtar Commodore Jemila ne a kashin kanta.

Ya bayyana cewa yayin bayaninta ta fadada lamarin ne a yadda ta fahimce shi amma ba da nufin ta wakilci hukumar “Navy” gaba daya ba.

 

Ya bayyana cewa hakan ya alakantu da wata kasa da ke makobtaka da Najeriya wacce kuma take da kyakkyawar alaka ta diplomasiyya da kasar Najeriya, yin magana kan ta daga hukumar “Navy” daban kana kuma fahimtar wani jami’i daga ma’aikatan ta Navy daban.

Don haka hukumar ta nesanta kanta daga wannan zargi da aka yi, kana kuma ta yaba da gudunmawar kasashen ketare da suke fafutukar yaki da safarar muggan makamai.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Hukumar “Navy” Ta Nesanta Kanta Daga Kalaman Cmmd. Jamila Kan Sojojin Chadi”