September 10, 2021

Hukumar NAFDAC ta hori yan Najeriya kan amfani da Manja

Daga Adam Muhammad

Hukumar kula da kuma sa ido kan abinci da magunguna na kasa (NAFDAC) ta zaburar da yan Najeriya kan amfani da abinci da magungunan da suke da illa ga lafiya.
Shugaban hukumar, Farfesa Majisola Adeyeye ne tayi bayanin a yayin wani taro a garin Ilorin.

Ta ce babban manufa na hukumar shine kiyaye yan kasa da amfani da abincin da ke da illa ga lafiyar su.

Ta bayyana cewa a kokarin su na samar da riba mai yawa a kasuwancin su, da yawan yan kasuwa na hada manja da “Azo dye” wanda ya kasance cikin sa akwai sinadaran da ke haifar cutar kansa duk don manjan su ya bad a kalar jah sosai.

Ta bayyana cewa da yawa yawan “Mai” da suke bacci (Manja ko farin Mai) suna da sinadaran da ke da illa ga lafiyar Dan Adam.

Ta kara kuma da cewa wasu lokuta akan yi safaran Manjan a cikin tankokin kalanzir wanda hakan matsala ce babba muddin mutane suka yi amfani da shi.

Ba a iya nan ta tsaya ba, ta yi jan kunne kan sayan magunguna daga wurin masu talla a titi inda ta nuna illar hakan da kuma horon mutane da sayan magani daga shagunan da suke da lasisi. Ta kuma yi bayanai kan illolin amfani da kodin (codaine) da kuma shan magunguna ba tare da shawarar likitoci ba.

Daga bangare guda kuwa tayi kira ga iyaye mata inda ta karfafe a bangaren shayar da jariran su had na tsawon shekaru biyu, ta bayyana cewa rashi shayar da jariri bisa kai’ida kan haifar da wasu cututtuka da kuma samar da yaro mai karamin kwakwalwa.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Hukumar NAFDAC ta hori yan Najeriya kan amfani da Manja”