September 8, 2021

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano tsamo gawar ɗan shekara 5 daga rijiya

Daga Baba Abdulkadir

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta ce, jami’anta sun tsamo gawar wani yaro mai kimanin shekaru 5 da ya mutu sakamakon faɗawa wata rijiya.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Saminu Abdullahi, ne ya faɗin hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar wa manema labarai,
Ya ce, yaron mai suna Yushau Usman ya cimma ajali sa ne a cikin rijiyar a garin Zangon Dinya da ke karamar hukumar Bagwai.
Sanarwar ta kuma ruwaito cewa, a daren Asabar da ta gabata ne ne ofishin hukumar na ƙaramar hukumar Bichi, ya samu kiran gaggawa da ƙarfe 08:30 inda wani magidanci Muhammad Usman, ya shaida musu faruwar lamarin.
Haka kuma hukumar ta ce, jami’an ta na sashen aikin ceto sun isa wurin ƙarfe 08:45, kuma bayan fi da shi ne suka tabbatar da cewa ya rasu, daga nan ne suka bai wa Dagacin garin Malam Yahaya Sule gawarsa.
Haka kuma hukumar ta ce, tana cigaba da gudanar da bincike kan rasuwar yaron.
SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Hukumar kashe gobara ta jihar Kano tsamo gawar ɗan shekara 5 daga rijiya”