April 25, 2023
Hukumar kare hakkin bil’adama ta Musulunci (IHRC) ta bukaci dan majalisar Labour na Burtaniya Barry Gardiner da ya nemi gafarar neman cire tutar Falasdinu mai dauke da “Kauracewa Haramtaciyar kasar Isra’ila” daga tagar ofishin su na Wembley, inda ta bayyana hakan a matsayin yunkurin rufe bakin masu goyon bayan ‘yancin Falasdinu.
