October 14, 2023

Hukumar ICPC zata gudanar da binciken yadda aka kashe N500b wajen gudanar da aiyuka a mazabun Najeriya

Rahoton Kamfanin Dillanci Labarai (NAN)


Hukuma ta musamman kan binciken laifuka a Najeriya ta ICPC ta bayyana cewa ta gama shiri tsaf don kaddamar da bincike da bibiyar yadda aka kashe zunzurutun kudaden da suka kai Naira biliyan 500 a mazabu daban-daban a fadin jihohin kasar wanda ya fara daga shekarar 2019.

Kakakin hukumar ICPC, Malama Azuga Ogugua itace ta bayyana haka cikin wani bayani da ta gabatar a birnin tarayyar Najeriya. Malama Oguguwa tace aikin zai kasance na hadaka don bibiyar yacce aka kashe adadin da aka ambata don aiwatar da ayyukan raya kasa guda 1,932.

Ta kara da cewa, jihohin da binciken zai fi mayar da hankali akai sun hada da jihohin Nasarawa, Gombe, Borno, Taraba, Benuwai, Kwara, Naija, Filato, Adamawa, Kogi da kuma Bauchi. Kari akan haka akwai jihohin Anambra, Bayelsa, Ondo, Katsina, Akwa-Ibom, Sokoto, Kebbi, Kano, Legas, Ebonyi, Imo, Ekiti, Edo da kuma birnin tarayya Abuja.

Malam Oguguwa tace, manufar wannan bincike shine tabbatar da aminci a hidimar al’umma da kuma habaka ingancin ayyuka da bankado duk wata badakala da aka yi wajen gudanar da aikin al’umma.

Malama Oguguwa ta kara da cewa hukumar zata mai da hankali kan hukumomi irin NEDC, PAP, NDDC, NSITF, NHIA HYPPADEC da kuma takororin su.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Hukumar ICPC zata gudanar da binciken yadda aka kashe N500b wajen gudanar da aiyuka a mazabun Najeriya”