November 23, 2021

Hukumar EFCC Na Gudanar Da Bincike Kan Tsohon Ministan Sufuri Femi Fani-Kayode

Daga Danjuma Makery


Hukumar dakile cin hanci da rashawa ta EFCC na gudanar da bincike kan tsohon ministan sufuri Femi Fani-Kayode.

Rahoton ya nuna cewa hukumar ta EFCC ta gayyaci tsohon minista Femi Kayode ne don bincikar sa kan zargin da take yi masa na buga takardun neman lafiya na bogi wanda ya gabatar a gaban wata babbar kotun tarayya a Legas don guje wa shariar sa dake gudana a kotun.

Rahotannin sun ce Femi Fani-Kayode ya isa ofishin hukumar ta EFCC da ke Legas bisa rakiyar lauyan sa da misalin karfe 1 na rana.

Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, Femi Fani-Kayode na amsa tambayoyi daga jami’an hukumar na EFCC kan tuhumar da ake yi masa.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Hukumar EFCC Na Gudanar Da Bincike Kan Tsohon Ministan Sufuri Femi Fani-Kayode”