June 4, 2023

Hukumar Ba da Agaji da Samar da ayyukan yi ga Falasdinawa ‘yan gudun hijira (UNRWA)na fuskantar rashin kudi.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana cewa Hukumar Ba da Agaji da Samar da ayyukan yi ga Falasdinawa ‘yan gudun hijira (UNRWA) na gab da durkushewar kudi, ya kira kasashen da ke daukar nauyin wannan hukuma da su cika hakkinsu.

A rahoton cibiyar yada labaran Falasdinu, Antonio Guterres ya bayyana a taron komitin musamman na UNRWA da aka yi a hedkwatar MDD dake birnin New York cewa, dukkanmu mun san muhimmiyar rawar da UNRWA take takawa a matsayin cibiyar samar da kudi wajen tallafawa mutane da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin. wannan hukuma na fuskantar matsalar kudi da kuma matsananciyar bukata.

Guterres ya jaddada cewa, a baya-bayan nan da yawa daga cikin kasashen da ke ba da tallafin UNRWA sun sanar da cewa za su rage tallafin da suke baiwa wannan kungiya ta kasa da kasa, lamarin da ke da matukar damuwa.

Ya ce gibin kasafin kudin hukumar ta UNRWA ya kai kimanin dala miliyan 75, amma duk da haka dole ne a ce tana dab da durkushewa.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Hukumar Ba da Agaji da Samar da ayyukan yi ga Falasdinawa ‘yan gudun hijira (UNRWA)na fuskantar rashin kudi.”