April 17, 2023

​Hukumar Abinci Ta Duniya Ta Tsaida Ayyukanta A Kasar Sudan Bayan An Kashe Ma’aikatanta Har 3

 

Hukumar abinci ta duniya WFP ta MDD ta bada sanarwan dakatar da dukkan ayyukanta a kasar na wucin gadi bayan da aka kashe ma’aikatanta 3 a fafatawan da ake tsakanin sojojin kasar da kuma dakarun daukin gaggawa na kasar ta Sudan a jiya Lahadi.

Tashar talabijin ta Al-Alam a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labarum reuyers na cewa, daractan zartarwa ta hukumar a Sudan Sindi Macain tana cewa a halin yanzu muna sanya ido don ganin lokacinda zaman lafiya zai dawo cikin kasar ta Sudan, amma a wannan halin mun dakatar da ayyukammu saboda ma’aikatammu basu da amincin da zasu ci gaba da ayyukansu na bada agaji ga dimbin mutanen kasar Sudan mabutaka ga taimakommu.

Labarin ya kara da cewa an kashe ma’aikatan hukumar ne a musayar wutan da aka yi tsakanin sojojin kasar a ranar Asabar, sannan wasu biyu kuma sun ji rauni a arewacin yankin Darfur.

Banda haka Macain ta kara da cewa ma’aikatanta guda 3 da aka kashe duk yan kasar Sudan ne, kuma an lalata jirgin saman hukumar wanda yake cikin tashar jiragen sama na birnin Khurtum.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Hukumar Abinci Ta Duniya Ta Tsaida Ayyukanta A Kasar Sudan Bayan An Kashe Ma’aikatanta Har 3”