May 31, 2023

HKI Ta Nuna Damuwarta Akan Kokarin Bunkasa Alaka Tsakanin Tehran Da Alkahira

Kafafen watsa labarun HKI sun bayyana cewa; Kawance da kasashen larabawa da Isra’ila take son kafawa domin fuskantar Iran, da mayar da ita saniyar ware, yana russhewa sannu a hankali.

Kafafen na ‘yan sahayoniya sun ce; Iran tana kokarin rusa kawancen da Isra’ila ta kafa da kasashen larabawa domin killace ta a siyasance da tattalin arziki.”

Tashar talabijin na “Channel 12’ ta HKI ta ce, a halin da ake ciki a yanzu Masar tana bunkasa alakarta da Iran daga kai mai kula da manufofinta zuwa matsayin jakada.”

Har ila yau tashar ta kuma kara da cewa; Alaka ta kyautata tsakanin Iran da Saudiyya, yanzu tana kokarin kyautata da Masar, nan gaba kadan shugabannin kasashen biyu za su sumbaci juna.”

Wannan dai yana zuwa ne bayan ziyarar da sarkin Oman Haitham Bin Tariq ya kawo Iran, kwanaki kadan bayan da ya ziyarci Masar a kokarin da kasashen biyu suke yi na bunkasa alakar diplomasiyya a tsakaninsu.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “HKI Ta Nuna Damuwarta Akan Kokarin Bunkasa Alaka Tsakanin Tehran Da Alkahira”