November 23, 2023

Hizbullah Tana Jana’izar Shahidai 5 A Yau Alhamis

 

A wannan Alhamis din an yi jana’izar shahidai biyar a garuruwa mabanbanta na kudancin Lebanon.

A garin Hula na yi jana’izar Shahid Ahmad Hassan Mustafa, sai kuma shahid Muhammad Hassan Ahmad Shari wanda aka yi tashi janazar a Kharbat-Salam.

A can yankin Biqa’a kuwa an yi janazar Muhammad Rabi’ah Audah, a garin al-khadra. Sai kuma a cikin birnin Beirut inda aka yi janazar Khalil Jawad Shuhaimi.

A garin Jiba’a kuwa an yi jazanar Abbas Muhammad Ra’ad wanda da ne ga shugaban ‘yan majalisar dkokin Lebanon masu wakiltar ‘yan gwgawarmaya, Muhammad Ra’ad

 

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Hizbullah Tana Jana’izar Shahidai 5 A Yau Alhamis”