Hizbullah Tana Goyon Bayan Sulaiman Faranjiya Ya Zama Shugaban Kasar Lebanon

Babban Magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasralalh ya ce;kungiyarsa tana goyon bayan Sulaiman Faranjiya akan ya zama shugaban kasa.
Shugaban kungiyar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi na tunawa da ranar ‘yan gwgawarmaya da su ka jikkata a wurin yaki, yana mai kara da cewa; Tunawa da wannan ranar yana nuni ne da sadaukar da kai, tare da cewa: “ Wajibi ne zuriyar da ta taso a wannan lokacin ta fahimci yadda dubban mutane a baya su ka shiga kurkuku na ‘yan sahayoniya.
Sayyid Nasrallah ya kuma kara da cewa; Yana kuma da kyau mu tunatar da wannan zuriyar ta yanzu akan gaskiyar Mukawama na cewa, ba ta barin ‘yayanta a cikin kurkuku a hannun ‘yan sahayoniya, za ta ‘yanto da su.”
Da yake Magana akan halin da HKI take ciki a yanzu, Sayyid Hassan Nasrallah ya ce: Abubuwan da suke faruwa a wannan lokacin,suna nuni ne da cewa HKI ta kusa zuwa karshe.”