January 12, 2023

Hizbullah Ta Bukaci Hukunta Mujallar Charlie Hebdo Ta Kasar Faransa

 

Kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ta bukaci gwamnatin Faransa da ta dauki matakin hukunta mujallar Charlie Hebdo ta kasarta

Mujallar Charlie Hebdo ta kasar Faransa ta sake daukan matakin wallafa maganganun batanci kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, bayan da ta buga wasu zane-zanen cin mutunci ga jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamene’i, sakamakon haka kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi kira ga mahukuntan Faransa a jiya Talata da ta hanzarta daukan matakin hukunta mujallar.

Mujallar Charlie Hebdo ta kasar Faransa dai ta yi kaurin suna wajen cin mutuncin da muzanta abubuwa masu alfarma na addinin Musulunci, inda a shekara ta 2015 ta wallafa zane-zanen batanci ga Manzon tsira, annabin rahama shugaban talikai Muhammadu dan Abdullahi {s.a.w}, don haka aka samu musulman da suka kaddamar da hari kan ofishinta da ke birnin Paris a ranar 7 ga watan Junairun shekara ta, 2015.

 

©hausa TV.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Hizbullah Ta Bukaci Hukunta Mujallar Charlie Hebdo Ta Kasar Faransa”