January 19, 2024

Hizbullah Na Cigaba Da Kai Hare-hare Akan Sojan Mamaya

A wata sanarwa da kungiyar ta Hizbullah ta fitar a ranar Alhamis ta ce ta kai hari akan sansanin sojan mamaya na “Barkatu-Risha” ta hanyar amfani da makaman da su ka dace kuma sun sauka inda aka auna su tare da yin barna.

Tun da fari kafafen watsa labarun israila sun ambaci cewa; An kai hari da makamai daga Lebanon akan sansanin na “Barkatu Risha’ dake yankin Jalilul-Garbi.

A gefe daya sojojin sahayoniyar sun kai hari da makaman Phursporus wnada aka haramta amfani da shi da duniya, inda su ka harba shi akan yankin Maisal-Jabal.

Bugu da kari, ‘yan mamayar sun kai wasu hare-hare da jirage marasa matuki a gefen garin Kaukabah a kudancin Lebanon.

A ranar Laraba mai dai kungiyar gwagwarmayar musuluncin ta Hizbullah ta kai wasu hare-haren akan cibiyoyi da sansanonin sojan mamaya ta hanyar harba makamai masu linzami 40 da kuma jirage marasa matuki 4.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Hizbullah Na Cigaba Da Kai Hare-hare Akan Sojan Mamaya”