September 16, 2023

Hizbullah A SHirye Take Ta Fuskanci Barazanar Isra’ial Da Amurka A Kudancin Asia

Wani babban jami’ii a kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa kungiyar zata yi amfani da makamanta don kalubalantar HKI da Amurka a yankin Kudancin Asia.

ya fadi  haka a wani taron makokin wafatan manzon All..(s) da kuma shahadar jikokinsu masu tsari Imam Hassan da Imam Aliyu bin Musa (a) a kudancin birnin Beirut babban birnin kasar a jiya Jumma’a.

Sayyid Hashem Safieddine ya kara jaddada cewa hizabullah ba zata yi amfani da makamanta don wata kungiya ko kuma mutanen kasar Lebanon ba, yace kungiyar tana shirin yaki nag aba wanda zai hadata ta HKI da kuma mamayar da takewa kasashen larabawa, da kuma makirce makircen Amurka a yankin.

A wani bangare da Jawabinsa Sayyid Hashem Safieddine yay i kira ga kungiyoyi da Jam’iyyun siyasa a kasar Lebanon da su shiga tattaunawa mai zurfi a tsakaninsu don zaben shugaban kasa, don wata rigima ta cikin gida ba zata taimakawa kowa a kasarba, kuma ba zai taba warware matsalolin da kasar take fama da su ba.

Kafin haka kungiyar ta Hizbullah da tokwarorinta na Falasdinawa, wadanda suka hada da Hamas da kuma Jahadul Islami sun sha alwashin yaki tare a duk lokacinda HKI ta takali daya daga cikinsu.

 

©Htv

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Hizbullah A SHirye Take Ta Fuskanci Barazanar Isra’ial Da Amurka A Kudancin Asia”