November 21, 2022

Hijabi Makami Ne Kuma Wasiyyar Sayyida Zainab Aƙeela (AS).

Hijabi Makami Ne Kuma Wasiyyar Sayyida Zainab Aƙeela (AS).

• Shi hijabi ɗaya ne daga manya manyan abubuwa dake tsorata maƙiyi kuma shaiɗani, domin sun sani sarai cewa Sayyida Zainab (AS) ta girgiza azzaluman zamanin ta ne a yayin da take sanye da hijabi, don hakane suke kokarin kawar da shi ta hanyoyi daban-daban, a da, da yanzu.

Kuma ki sani ƴar uwa mai daraja duk wani shaiɗani (na wancan zamani da na yanzu) yana tsoron mace data lazimci sanya hijabi, a duk sanda ya ganki sanye da hijabi sai ya cire rai akanki tare da cewa wannan ba hajarmu bace”, Saɓanin wacce zai ga jikin rabi a rufe rabi.

©Sheikh  Emran Haruna  Darussalam.

SHARE:
Makala 0 Replies to “Hijabi Makami Ne Kuma Wasiyyar Sayyida Zainab Aƙeela (AS).”