October 24, 2022

Hawan jini cuta mai kisan Mummuke Saboda yadda yake mummunan Lahani ga Jikin dan Adam Batare da Nuna Alamaba.

Duba hanyoyi 14 da hawan jini ke yin mummunan lahani ga sassan jiki kafin a ankare.

1. Rarake jijiyoyi ko hanyoyin jini: Lafiyayyun jijiyoyin jini suna da ɗabi’ar balan-balan ne, wato suna iya talewa ko buɗewa yayin da zuciya ta bugo jini sannan su koma yadda suke. Amma idan aka samu hawan jini, ƙarfin bugun jinin na wuce yadda jijiyar jinin za ta iya jurewa. Saboda haka, yau da gobe, bugun hawan jinin a cikin jijiyoyin zai rarake cikin jijiyoyin. Rarakewar jijiyar jinin zai haifar da raguwar talewa ko buɗewa don wucewar jini cikin sauƙi.
Haka nan, da zarar cikin jijiyoyin sun rarake, kitse zai kwanta a duk gurbin da jijiyar ta rarake. Rarakewar jijiyoyin jinin, tare da kwanciyar kitse a cikin jijiyoyin jinin zai sa jijiyoyin su yi tauri tare da cushewarsu.

2. Bullin jijiyar jini: Hawan jini na iya bunƙura wani sashi na jijiyar jini har ta yi bulli. A duk lokacin da jijiyar jini ta yi bulli kuwa, ingancinta na raguwa, kuma tana iya fashewa a kowanne lokaci yayin da zuciya ta harbo jini. Fashewar jijiyar zai kawo ɓallewar jini a sassan jiki, musamman a jijiyoyin jini na kusa da zuciya da ƙwaƙwalwa.

3. Cutar jijiyoyin jinin zuciya: Kamar yadda kowanne sashin jiki ke da jijiyoyin da ke kai masa jini, haka ma zuciya da kanta tana da jijiyoyin da suke ba ta jini. Kitse kan taru a cikin jijiyoyin sai ya toshe jijiyar jinin. Wannan zai kawo cikas wajen gudanar jini ga zuciya, sannan ya haifar da ciwo ko zafin ƙirji da kuma rikicewar bugawar zuciya.

4. Bugun zuciya: A yayin da tittika ko diddigar kitse ta toshe wata daga cikin jijiyoyin jinin zuciya, hakan zai kawo ƙarancin iskar oksijin ga tsokar zuciya – sai zuciyar ta buga – aikinta ya tsaya.

5. Cutar jijiyar jini nesa da zuciya: Ƙunci ko toshewar jijiyar jini na iya faruwa a can nesa da zuciya, misali, a ƙafa wanda ke iya kawo ciwo ko damƙa, musamman yayin tafiya, a dambubu ko sha-raɓa.

6. Kassarewar zuciya: Hawan jini na sa jijiyoyin jini su yi tauri kuma su matse. Saboda haka, sai zuciya ta yi aiki tuƙuru don harba jinin zuwa dukkan sassan jiki. Aiki tuƙuru, ba dare ba rana, zai sa zuciya ta yi rauni har daga ƙarshe ta kassare.

7. Buɗewar zuciya: Ma’ana, aikin zuciya tuƙuru, domin ta harba isashshen jini, zai sa ta riƙa buɗewa, wato ta riƙa ƙara faɗi daga ciki. Kuma ƙaruwar faɗinta na nufin raguwar ingancin aikinta.

8. Shanyewar ɓarin jiki: Hawan jini shi ne kan gaba wajen haddasa shanyewar ɓarin jiki. Wani sashi na ƙwaƙwalwa zai fara mutuwa saboda rashin zuwan iskar oksijin sakamakon fashewa ko toshewar wata jijiyar jini a wani ɓari na ƙwaƙwalwa.
Alamun shanyewar ɓarin jiki akwai: karkacewar baki, rauni ko shanyewar hannu ko ƙafa, karyewar harshe, da sauransu.

9. Gigi/ruɗewa: Hawan jini na kawo canjawar aikin ƙwaƙwalwa saboda matsalar gudanawar jini a ƙwaƙwalwa. Wannan zai kawo gigi, ruɗewa, da ƙarancin nutsuwa a ayyukan yau da kullum.

10. Kassarewar ƙoda: Hawan jini shi ne na biyu a jerin sanadan da ke kassara aikin ƙoda. Tauri da matsewar jijiyoyin jini, ga masu hawan jini, na kawo cikas a ayyukan ƙoda kamar tace guba daga jini zuwa fitsari, daidaita ruwan jiki da sauransu.

11. Matsalar gani: Hawan jini na rage gudanar jini a ido wanda hakan kan lahanta jijiyar laka ta ido, wacce take sadar da saƙonnin gani daga ido zuwa ƙwaƙwalwa domin fassarawa. Lahani ga jijiyar lakar ido zai kawo raguwar gani ko makanta gaba ɗaya.

12. Matsalar saduwa da iyali: Kamar yadda hawan jini ke rage gudanawar jini a dukkan sassan jiki, haka ma yake rage gudanawar jini a azzakari da farji yayin saduwa. Sannan matsalolin saduwa da iyali su biyo baya.

13. Raunin ƙashi: Fitsarin masu hawan jini kan kasance ɗauke da sinadarin kalsiyam (calcium) a ciki fiye da ƙima. Ana ganin yiwuwar hawan jinin ne ke sa jiki fitar da sinadarin kalsiyam zuwa cikin fitsari. Kuma, kasancewar kalsiyam muhimmin sinadarin ginin ƙashi ne, raguwarsa a jiki yau da gobe na kawo haɗarin karayar ƙashi, musamman ga tsofi.

14. Katsewar bacci: Hawan jini na sa hanyoyin iska na maƙogaro su saƙi, wannan zai kawo rufewar maƙogaro yayin bacci. Rufewar maƙogaron zai hana shaƙar iska wanda hakan zai sa mutum farkawa daga bacci ba shiri.

©Physiotherapy Hausa

SHARE:
Kiwon lafiya 0 Replies to “Hawan jini cuta mai kisan Mummuke Saboda yadda yake mummunan Lahani ga Jikin dan Adam Batare da Nuna Alamaba.”