April 17, 2023

Hauhawar farashin kayan masarufi a Najeriya ya kai kaso 22.04

Ofishin dake fitar fa alkaluma na kididdigar tattalin arziki a Najeriya NBS ya sanar jiya Asabar 15 ga wata cewa, mizanin karuwar farashin kayayyakin abinci da na sauran bukatun yau da kullum a kasar ya kai kaso 22.04 a watan jiya na Maris.

Ofishin ya ce an samu karuwar kashi 0.13 cikin 100 idan aka kwatanta da farashin kayayyakin a wata Fabrailun 2023.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da karin bayani a kan rahoton hukumar ta NBS.

A cewar rahoton, ta fuskar kayan abinci kadai farashi ya tashi daga kaso 24.35 a watan Fabrailu zuwa kaso 24.46 a watan Maris.

Karuwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya cikin gaggawa ya tilastawa babban bankin kasar kara yawan kudin ruwa mafi yawa a tsakanin shekaru 20, lamarin da ba a saba ganin hakan ba.

A kokarin dakile annobar hauhawar farashin kayan ne ma babban bankin tarayyar Najeriya CBN a cikin watan jiya na Maris ya daga darajar bashi zuwa kaso 18 cikin 100.

Kamar yadda taswirar mizanin kayayyakin da suka yi tashin gauron zabi ya nuna, bangaren kayan abinci da abubuwan sha na kwalba farashin su ya karu zuwa 11.42 idan aka kwatanta da watannin baya, sai farashin gidaje da kudaden haraji na ruwa da wutar lantarki da gas ya kai 3.69, sai farashin kayan tufafi da takalma wanda ya kai kaso 1.69, sai kuma bangaren sufuri ya tashi zuwa kaso 1.43 cikin dari, yayin da kuma farashin kayan kawa na gidaje da kayan gini ya kai kaso 1.11.

A sakamakon wanann rahoto ne tashar CRI ta tuntubi Dr. Aliyu Tahir, mataimakin darakta na tsangayar nazarin harkokin bankunan musulunci a jami’ar Bayero, ko me yake jin ya haifar da rashin daidaiton farashin kayayyakin a Najeriya?

Dr. Aliyu Tahir ya ce, “Daga cikin abubuwan da suke haifar da hakan dai akwai batun karin kudin ruwa da babban bankin kasa ke fitarwa wato Interest Rate, wanda da shi bankunan kasuwanci ke saka nasu ribar da za su caja daga wurin wadanda suke baiwa rance, kuma hakika wannan kason shi kansa ya haura daga kaso 17 zuwa wajen 18, to amma dai kada a manta yanayin tattalin arzikin duniya shi ma kansa ya taka rawa tsadar man fetur da man gas duk suna janyo abubuwa su tashi sosai, kuma a bisa nazari, zai yi wahala abubuwa su yi kasa a cikin wannan watan ma na Afrilu, daman dai duk lokacin da kaya suka tashi saukowar su na da mutukar wahala a lokaci guda.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Hauhawar farashin kayan masarufi a Najeriya ya kai kaso 22.04”