April 13, 2023

Hauhawar farashin kaya a Ghana ta ragu zuwa kashi 45 a watan Maris.

Rahotanni daga kasar Ghana na cewa, an samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki a kasar da kashi 45 cikin dari a watan Maris, wanda shi ne karo na uku a jere da aka samu raguwar farashin kaya tun a watan Mayun 2021, bayan faduwar farashin da aka samu a watan Janairu.

Hukumar Kididdiga ta Ghana (GSS) ta bayyana a jiya Laraba cewa, an samu raguwar kaso 7.8 a watan Maris, kan kashi 52.8 cikin 100 da aka samu a watan da ya gabata.

Jami’in kididdiga a hukumar ta GSS, Samuel Kobina Annim ya bayyana a yayin taron hukumar na wata-wata cewa, raguwar hauhawar farashin kayayyaki da aka samu.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Hauhawar farashin kaya a Ghana ta ragu zuwa kashi 45 a watan Maris.”