August 10, 2021

HATSARIN MOTA YA HALLAKA MUTANE 4 DA KUMA JIKKATA MUTUM 6

Daga Muhammad Bakir Muhammad

A yammacin ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta hadarin motan ya wakana a kan hanyar Dogon-Kuka zuwa Damaturu na jihar Yobe.

Hatsarin motan yayi sanadin mutuwar mutun hudu a inda wasu mutum shida kuma suka jikkata. Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 5 na yamma inda ya ritsa da wasu fasinjojin wata  mota Hayas kirar Toyota.

Hukumar kula da zirga-zirgan ababen hawa a jihar ta Yobe sun tabbatar da aukuwar lamarin inda suka tabbatar da cewa mutum hudu sun rasa rayukansu inda kuma wasu shida suka ji munanan raunuka.

Mai magana da yawun hukumar ya tabbatar da manema labarai cewa gudu ba bisa ka’ida ba shine ummul abaisin faruwar hatsarin sannan kuma ya bayyana cewa wadanda abin ya shafa tuni aka dauke su zuwa Babban asibitin kwararru da ke garin Damaturu; Babban birnin jihar ta Yobe domin bincike da taimakon gaggawa ga wadanda abin ya ritsa da su.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “HATSARIN MOTA YA HALLAKA MUTANE 4 DA KUMA JIKKATA MUTUM 6”