September 26, 2021

Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutane 2 A Jahar Ondo

Musa Isah Muhammad


A yau Lahadi ne wasu mutane biyu suka rasa rayukan su a hatsarin da ya faru tsakanin wata Mota da kuma Dan achaba da ke bisa babur.

Hatsarin ya faru ne a garin Akure, babban birnin jahar Ondo, kuma ya faru ne a kan babban titi na asibiti.

Rahotanni dai sun nuna cewa mutane biyu da ke bisa babur din sun rasa ruyukansu take a yayin da motar ta buge su ta baya, sai dai kuma shi Dan achaban wanda ya kasance cikin mutane uku da ke kan babur din ya samu nasarar tsira da rayuwarsa tare da raunuka.
Hatsarin ya haifar da cinkoson ababen hawa.

Wadanda suka shaida wa idanun su abinda ya faru sun bayyana cewa matukin motar ya kasance yana gudu ba bisa ka’ida ba wanda hakan ne yayi sanadin auwar lamarin.

 

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutane 2 A Jahar Ondo”