November 1, 2023

Sayyed Hassan Nasrallah Zai Gabatar Da Jawabi A Ranar Juma’a Mai Zuwa

Bangaren Watsa labaru na kungiyar ta Hizbullah ta fitar da sanarwa a jiya Lahadi dake cewa; Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah sayyid Hassan Nasrallah zai gabatar da jawabi na girmama shahidai a ranar juma’a 3 ga watan Satumba.

jawabin na Sayyid Hassan Nasrallah zai kasance ne a karkashin girmama shahidan da su ka kwanta dama a farmakin da ake kai wa HKI wanda Hizbullah din ta bai wa sunan; Shahidan da su ka kwanta dama akan hanyar kudus.

Wannan shi ne karon farko da babban sakataren kungiyar ta Hizbullah zai gabatar da jawabi tun bayan farkewar da HKI ta shelanta akan Yankin Gaza.

Sai dai tun ranar 8 ga watan Oktoba ne mayakan kungiyar ta Hizbullah su ka fara kai wa sojojin HKI hari, inda ya zuwa yansu sun kashe tare da jikkata fiye da 40.

 

©Voh

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Sayyed Hassan Nasrallah Zai Gabatar Da Jawabi A Ranar Juma’a Mai Zuwa”