April 28, 2023

HASKEN MA’ABOCIN ZAMANI (ATFS).

 

Sheikh Nazaar (H) yace: “Malamin mu kuma Marji’in addini Sheikh Wahid Alkurasani (DZ) yana da wani kalma da yake faɗa akan wannan sha’ani, yana yawan cewa: “Mutumin da ke so rana ta haska shi, wajibi ne a gare shi ya fita daga tsakanin gini da ƙarƙashin baranda (wato ya kasance a wajen gida), amma wanda ya kasance yana cikin gida tsakanin gini da ƙarƙashin baranda bazai taɓa yuwuawa hasken rana ya isa gare shi ba”

Tofa haka nan ludufin Imam Mahdi (Atfs) game da haduwa dashi yake, domin shine hasken wannan duniya, wanda hasken shi ke haskaka zukata, wanda ke son hasken Imam ya haskaka shi wajibi ne sai ya bar tsakanin ginin hijabi da zunubi, a yayin nan ne hasken zai isa gare shi.

✓ Ya Allah ka haskaka zukatan mu da hasken Imam Mahdi (Atfs).

اللهم عجل لوليك الفرج

©SHEIKH  E m r a n D a r u s s a l a m.

SHARE:
Makala 0 Replies to “HASKEN MA’ABOCIN ZAMANI (ATFS).”