Harin Ofishin Jakadancin Azerbaïdjan A Tehran, Bai Da Alaka Da Ta’addanci

Ministan harkokin wajen kasar Iran, ya bayyana cewa harin da wani mutum ya kai ofishin jakadancin kasar Azerbaijan dake birnin Tehran, ba shi da wata alaka da aikin ta’addanci.
Bayan bincike an gano cewa mutimin da ya kai harin na ranar Juma’a, ya aikata hakan ne bisa wasu dalilai da suka shafe shi masu nasaba da iyalinsa, inji Amir Abdolahian.
Ya kara da cewa tuni shugaban kasar ya bayar da umanin gudanar da bincike kan lamarin ta fuskar shari’a da kuma jami’an tsaro.
Ministan harkokin wajen kasar ta Iran, ya ce ya tattauna da takwaransa an Azerbaijan din, kan batun kuma sun amince jakadan na Azerbaijan zai koma bakin aikinsa a Tehran.
A jiya ne dai mutumin wanda mutum, ya farmawa ofishin jakadancin na Azerbaijan da bindiga inda nan take ya kashe jami’in tsaro guda tare da raunata wasu guda biyu, kafin jami’an tsaro su cafke shi.