September 16, 2021

Harin Jiragen Yaki Kan Kauyukan Yobe: Gwamna Buni Ya Bukaci Fadada Bincike

Daga Muhammad Bakir Muhammad

 

Mai girma gwamnan jahar Yobe Mai Mala Buni ya nemi a fadada bincike don gano abinda ya sabbaba harin da jirage suka kai wasu kauyuka a jahar ta yobe wanda ya haifar da asarar rayuka da dama. Rahoto ya nuna cewa harin ya fi barna ga kauyen Buhari dake karamar hukumar Yusufari da ke jihar Yobe.

Mai magana da yawun hukumar sojin sama, A C Edward Gabkwet ya nesanta hukumar sa da aukuwar lamarin tun farko.

A wani bayanin da Daraktan yada labarai Mammam Mohammed ya bayyana cewa gwamna Buni jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukan su sanadin faruwar lamarin.

Kana kuma gwamnan ya bayyana cewa duk da cewa faruwar lamarin zai iya kasancewa hadari ne ko kuma bisa kuskure duk da haka zasu hada hannu da hukumomin tsaron don zakulo musabbabin faruwar lamarin.

Baya ga haka, gwamnan ya bada umarni ga mai bashi shawara kan harkokin tsaro da ya aiwatar da bincike da kuma hadin gwiwa da hukumar sojin sama tare da jami’ai na musamman don gano lamarin.

Ya kuma kara da cewa wajibin su ne su tabbatar da kaucema sake faruwar haka anan gaba kuma dole ne bada kariya ga rayukan al’umma. Ya kara bada tabbacin cewa gwamnatin sa ta shirya tsaf don yin aiki da Hukumomin tsaro don tabbatar da zaman lafiyar a jahar ta Yobe.

Daga karshe kuma ya bada umarni ga asibitocin garin Geidam da damaturu kan bada magunguna kyauta ga wadan da suka jikkata sakamakon harin.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Harin Jiragen Yaki Kan Kauyukan Yobe: Gwamna Buni Ya Bukaci Fadada Bincike”