March 9, 2023

Harin jami’an sojan sama ya halaka yara da Mace mai juna a Kaduna

 

Rahotanni na nuna cewa wani hari da jami’an sojan sama suka kai ya kuskure inda ya halaka yara biyu da wata mace mai dauke da juna a jihar Kaduna.

Lamarin dai ya faru ne a kauyen Sabon Gida da ke gundumar Fatika ta karamar hukumar Giwa a jihar Kadunan Najeriya.

Rahotanni sun ce harin dai ya yi niyar farmakar wasu yan ta’adda ne da ke sansani a wani daji da ke kusa da kauyen.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata da misalin karfe 5 na maraice..

Harin ya kashe mutane 3 kana kuma ya raunata wasu mutane 5.

 

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Harin jami’an sojan sama ya halaka yara da Mace mai juna a Kaduna”